Labarai

TONON SILILI: Shugaba Buhari Zai Fara Yi Wa Maciya Amanarsa Korar Kare

Advertisment

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

Rahotonnin sirri sun tabbatar mana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar tarihi a Njeriya na wurin sallamar na kusa da shi, kuma wadanda suke rike da madafan iko.

Hakan ya samo asali ne don magance ire-iren matsalolim da ake samu na matsalar tsaro da kuma shirin ruguza tattalin arzikin Nijeriya, duba da yadda aka samu ‘yan handama da babakere duk da irin kokarin da Shugaban yake yi na dawo da tattalin arzikin kasa.

A harkar tsaro kuma akwai yiwuwar zakulo wadanda keda hannu a wurin haddasa rashin tsaro a Nijeriya.

Rahoton mu ya kara tabbatar mana da cewa, bayan baiyanawa al’umma wadanda ke da hannu a wurin kawo matsaloli a wannan kasar, za kuma a dakatar da wadansu manya a Nijeriya daga karagar mukamansu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button