Gwamnatin Kaduna ta dauki ma’aikata aiki a Jami’ar KASU, taki biyan su albashi na tsawon shekaru uku
Wasu malamai da ma’aikata a Jami’ar jihar Kaduna KASU sun koka da yadda suka ɗauki tsawon shekaru uku suna aiki amma ko sisi ba a taɓa biyan su a matsayin albashi ba ballanta na alawus ko kudin hutu.
PUNCH ta buga cewa wadannan ma’aikata sun bayyana cewa an cire sunayen su daga jadawalin sunayen ma’aikatan Jami’ar da ake biya albashi.
Ma’aikatan sun ce Jami’ar bata biyan su albashi saboda tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya maida al’amuran Jami’ar ƙarƙashin ofishin sa, komai za ta yi sai ya sa hannu, premium times hausa na ruwaito
Ma’aikatan sun ce basu cikin tsarin inshorar lafiya saboda basu da takardan shaidan biyan su albashi.
Wani cikin ma’aikatan da baya so a fadi sunnan sa ya ce ya yi watanni 22 yana aiki ba a biya shi albashi ba.
“Bayan an dauke ni aiki sai na samu karin girma zuwa matsayin mataimakin babban malami amma babu albashi. Daga nan wasu daga cikin mutanen da muka samu aiki tare suka fara samun albashi a watan Fabrairu amma mu kuma shuru.
Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Adamu Bargo ya ya ce jami’ar na karkashin ikon gwamnatin jihar Kaduna ne, gwamnatin ce ke biyan duk ma’aikatan jami’ar albashi.
Bargo ya yi kira ga duk ma’aikatan da basu samun albashi da su kara hakuri cewa jami’ar na kokarin warware wannan matsala nan ba da dadewa ba.