Labarai
Yanzu – Yanzu : Obaseki ya cire rufin Majalisar Dokokin Edo
Advertisment
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ke kudancin Najeriya ya cire duka rufin majalisar dokokin jihar da zimmar hana kowa zama cikin ginin majalisar.
Wannan na zuwa ne bayan da โyan sanda a jihar suka yi wa ginin majalisar jihar kawanya wadda ke Benin babban birni jihar.
Kakakin gwamnan Obaseki ya shaida wa BBC cewa ya yi hakan ne da nufin hana wasu ‘yan siyasa ciki har da gwamnan wata jiha cika burinsu na kwace jihar lokacin da ake daf da gudanar da zaben gwamna a jihar.
Gwamman jamiโan tsaro ne suka sanya shinge a wajen ginin majalisar.
Kakakin โyan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa jamiโan sun je ne da nufin kare rikicin da ake zaton zai iya tashi.
Rikicin siyasa na kara ฦamari a jihar da aka tsara yin zaben gwamna a watan Satumbar gobe.
Rahotanni sun ce babu dai kowa a cikin ginin majalisar. Kimanin mutum 200 ne suka yi carko-carko a wajen ginin majalisar, kuma mafi yawansu magoya bayan gwamna mai ci ne.
Alโamura na kara rikicewa tun bayan tuษe mataimakin kakakin majalisar Yekini Idaiye da aka yi a ranar Laraba kan zargin shi da karya doka.
A baya ya fito ฦarara ya nuna goyon bayansa ga abokin hamayyar gwamna mai ci.
A sauya shekar da yayi na ban mamaki a watan Yuni, Gwamna Godwin Obaseki, ya sauya daga jamโiyya mai mulki ta APC zuwa babbar jamโiyyar hamayya ta Bbchausa.com na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com



