Ana zargin masarautar Kano da sayar da masallacin Idi
Al’ummar Darmanawa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya sun zargi masarautar Kano da sayar da masallacin Idi da ke yankin.
Mazauna unguwar ta Darmanawa Lay Out sun ce a ranar Litinin da Talata sun wayi gari da ganin wasu mutane suna yanka filin masallacin Idin duk da kwamitin da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kafa domin samar da matsaya kan filin.
Kungiyar ci gaban unguwar ta ce abin da ya fi ba su mamaki shi ne yadda aka aika ‘yan sanda filin domin bayar da tsaro a yayin da mutanen ke rarraba filin na Idi.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito a shafinta .Shugaban kwamitin kula da masallacin idin, Barista Tijjani Yahaya, ya shaida wa BBC Hausa cewa mutanen da suke gididdiba filin masallacin sun yi ikirarin cewa filin mallakin masarautar Kano ne.
“Sun yi ikirarin cewa wannan harabar filin masallaci na wannan unguwa da muke zaune a cikinta, Darmanawa, mallakar masarautar Kano ne. Dauka da kuma rarraba wannan fili Idi a mayar da shi zuwa fulutai domin a sayar wa mutane,” in ji shi.
Ya kara da cewa sun je gaban Sarkin Kano inda suka yi kira a gare shi ya tsawatar wa mutanen da ke hankoron karkasa filin kuma ya bayar da umarni a binciki wannan magana sannan “ranar 6 ga watan daya na wannan shekara muka rubuta takarda muka kai fada kuma mun samu tabbaci ta isa ga martaba tun da har an kawo mana sitamfi.”
Sai dai Barista Yahaya ya ce sun yi mamaki da suka wayi gari suka ga ana yanka filin duk da tabbacin da suka samu daga sarkin na Kano.
A cewarsa, har yanzu ana ci gaba da yanyanka filin yayin da jami’an tsaro suke sanya ido kan masu aikin.
Sai dai masarautar ta Kano ta musanta cewa tana rarraba filin na Idi.
Ta ce Sarkin na Kano ya umarci da a dakatar da raba filayen amma ba su da masaniyar cewar ana ci gaba da aikin raba filayen kuma ba ita ta sa aka girke ‘yan sanda a filin ba.
Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, mataimakin Magatakardar masarautar, ya shaida wa wakilinmu Khalifa Dokaji cewa sarkin Kano ya bai wa mutanen unguwar damar gabatar da shaidun da za su nuna cewa filin mallakinsu ne.
“Wadannan mutane sun kawo kokensu gaban mai martaba sarkin Kano, amma ai sarki ya kafa kwamiti ya ce a je a bincika. Kuma dukkan takardu da suka yi bayanai cewa an yi magana da marigayi sarkin Kano, ai an ce su kawo su. Da wadannan takardu [sarki] zai amfani su zama hujja wajen yanke hukunci,” a cewarsa.
Wannan batu na faruwa ne a yayin da al’ummar jihar Kano ke ci gaba da kokawa kan yadda gwamnatin ta sayar da wasu bangarori na filin babban masallacin Idi na Kano da ke Kofar Mata ga ‘yan kasuwa, da na wasu sassan masallacin Juma’a na Fagge.
Wani batu da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ke cewa ya saba da dokar hakkin mallakar kasa, musamman wuraren da al’umma ke amfana da su.
Sai dai gwamnatin ta Kano ta ce tana sayar da filyae ne domin bunkasa tattalin arzikinta.