Labarai

Zazzafan martani zuwa ga tsohon sarki Sanusi Lamido daga barista sheikh ishaq

Barista sheikh ishaq yayi martani akan maganar tsohon sarkin Kano sanusi lamido sanusi II akan maganar adalci.

Shine shine malamin yake mayar da magana akan irin maganar da shi tsohon sarkin kano sanusi akan irin shawarar da sunka bada akan a cire tallafin man fetur Sheikh ishaq yana cewa.

“Shiyasa dazu naji wani yana magana akan adalci tsohon sarkin Kano yana magana adalci, adalci, zalunci, zalunci, su ba su suka bada shawarar a cire tallafi ba, basu jefa talakawa cikin bala’i ba, wannan adalci su sukace a saki dala tayiwa kanta farashi wannan ya zamo sanadiyyar shigar mutane cikin bala’i adalci ne.

Abubuwa da yawa wanda su mutane sun san ba adalci sukayiwa mutane a rayuwarsu ba sai dai kawai suzo su dinga gayawa mutane abinda sunka ga dama, talakawa a sasu mafisa a sasu bala’i .

Akan rikici yaron nan yanusa yellow waye ya mayar da shi wannan garin shi wannan adalci ne, a duk lokacin da arna sunka fito da ra’ayi sai ka goya bayansu baka goyi bayan yan uwanka musulumi ba shi wannan adalci ne.

Asali filin idi da aka zo aka rushewa talakawa aka sanya su cikin bala’i akan rabasu da jarinsu da kasuwancin su suwaye sunka sayar da shi, waye ya taso ya hada baki a sayar da talakawa waye? ya fito yace da sa hannun su anka sayar da shi wannan abun ba dai-dai bane a duk lokacin baka da baki kazo kana maganar zalunci zalunci.

Malam Sheikh barista ishaq ya ƙara da cewa ya kamata idan mutum zaiyi maganar adalci yayi adalci ta ko wace fuska, tunda da ku anka hada da tsohuwar gwamnati kunka saida wannan filin idi da za’a rushewa ya kamata ku shiga kuyi wani abu to haka dan Nijeriya yake shi duk abinda yayi na zalunci ba zalunci bane, a’a shi abinda a biyan buƙatar sa bai samu ba shine zalunci – inji sheikh ishaq.

Ga bidiyon nan ku saurari sauran.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button