Manoman Rani Za Su Samu Tallafin Noma Na Gwamnatin Tarayya Da Kashi 50 Cikin 100


Manoman Rani Za Su Samu Tallafin Noma Na Gwamnatin Tarayya Da Kashi 50 Cikin 100
Daga wannan shekara da muke ciki ta 2023 zuwa 2024, gwamnatin tarayya na shirin bayar da tallafi noman rani na kimanin kashi 50 cikin 100.


Ministan aikin noma da samar da wadataccen abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyna haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar tasa ta wallafa a shafinta na sada zumunta.
Kyari ya sanar da cewa, wannan buri na daga cikin ajandar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma matakan da Gwamnatin Tinubun ke dauka, domin magance hauhawar farashin kayan masarufi a fadin kasar nan baki-daya.
A cewar Ministan, bayar da tallafin zai shafi daukacin kayan aikin noma da suka hada da Iri na noma, takin zamani da kuma maganin feshi da za a raba wa manoman.
Kazalika Ministan ya bayyana cewa, taimakon da ake samu daga wurin Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB), a kan aikin noman rani na shekarar 2023 zuwa shekarar 2024, an gabatar da shi ne a karkashin shirin habaka aikin noma na (NAGS-AP).
Wani labarin : Muna Bukatar a Gaggauta Bincike akan Harin Bom da Sojoji suka yi wa Masu Maulidi – Kungiyar Agaji
Kungiyar agaji ta munazzamatu fitiyanul Islam reshen babban birnin tarayya Abuja
Tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta jgaggauta bincike da hukunta duk wanda yake da hannu a wannan mummunar aika aika na jefa bom a gurin Taron Maulidi a Garin tundun faira a jihar Kaduna
A Wata Sanarwa da Kungiyar ta fitar ta Hannu Mukaddaahin Jami’in Watsa Labarai na Kungiyar Muhammad Sani Yusuf Kungiyar Agajin ta Kara da Cewa lallai baza a lamunci kashe mutane kamar kiyashiba sannan Hukuma bata yi wani abu akai ba
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






