Labarai

Yadda zaka cika tallafin Karatu Na Gwamnatin tarayya

Bayan Kun Shiga link zaku ga inda zaku kirkiri profile naku, za’a bukaci ku saka Gmail address, password Wanda Baku manta dashi ba, sannar surname, First name, middle name idan akwai, Sai phone number. Sannan ku zabi federal government scholarship.

Kuna Gama cikawa Sai KUyi submit zai kaiku shafin Gama inda zaku ga Gmail address naku saiku saka password Wanda kuka kirkira a baya kuyi login zai kaiku sabon shafi.

Anan zaku ga ya Nuno muku welcome da sunan ku Wanda kuka cike a kirkirar profile to saiku ja screen na wayar ku zuwa kasa zaku tarar da Wajen profile completion status.
Wanda akwai Wajen bio-data da Kuma Wajen parent next of kind info.
To dukkan su Sai Kun cike su..

Zaku Fara daukar bio-data Wanda zaku ga ya Nuno muku 31% ku Gama cike shi sannan a kasa akwai click here to complete Sai ku Danna Nan ku jira ya Gama budewa.

Idan ya Gama budewa zaku ga anbukaci da kuyi upload na photo saiku Danna zai kaiku cikin gallary naku saiku zabi photo da kuke son dorawa Amma dole ne photo ya kasance baifi 50kb ba, Daga Nan Sai inda zaku saka NIN number ku, sannan zaku ga sunan da kuka saka idan Kuna son gyarawa saiku gyara, Sai kuga Wajen da zaku zabi gender wato jinsin ku, Sai Wajen da zaku cike matakin karatun da kuke son cikewa Wanda aka yiwa lakabi da academic level applying for, sannan Sai Wajen da zaku saka shekara haihuwar ku, Sai jaharku da karamar hukumar ku da address na unguwar ku da postal code na garin ku, zaku iya duba postal code a Google yadda zaku Yi shine ku rubuta sunan garin ku sannan da postal code misali: Hadejia postal code to zasu Baku na wannan garin, daga Nan Sai Wajen da zaku saka ko Kuna da aure ko baku, shikenan daga can kasa zaku ga save Sai ku Shiga Nan

Bayan kuyi save Sai ku Shiga na kasa wato parent/next of kin info.
Anan zaku cike sunan mahaifi, sana’ar sa, number wayarsa, Gmail address nasa sannan daga kasa zaku saka dangantaka ma’ana Wanda ka cike mahaifi ne kokuma mahaifiya.
Sannan Sai next of kin info Wanda yake daukar nauyinka.

Shima anan zaku cike sunansa, sana’ar sa, number wayarsa, address na inda yake zaune, Gmail address nasa, Sai ku zabi dangantakar dake tsakanin ku ma’ana Yaya ne namiji ko mace, miji ne ko Mata dasauransu. Daga Nan saikuyi save.
Shikenan Kun Gama cikawa,
Muna muku fatan nasara.

APPLY NOW

Sources: Ginsau

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button