Mutanen Tudun-Biri sun mutu da kalmar shahada – Tinubu
Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a lokacin da yake jaddada ta’aziyarsa ga ‘yan uwan mamatan a fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi da ya kai masa ziyara a wannan Litinin a birnin Maiduguri.
‘Yan Najeriya ne da ke da kwakkwaran imani, kuma a lokacin ibtila’in, sun kasance suna furta kalmar shahada. Allah ya tausasa zukatan ‘yan uwansu, yayin da kasarsu ke cikin bakin-cikin rasuwarsu. Allah ya sa sun huta. Inji shugaba Tinubu.
Kazalika shugaban Najeriya ya lashi takobin cewa, gwamnatin tarayya za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da tallafi da kulawa ga iyalan daukacin ‘yan kasar da matsalar tsaro ta shafa a jihar Borno, jaridar rfihausa na ruwaito.
Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa bangaren tsaro muhimmanci tare da samar da kyakkyawan yanayi da kayayyaki ga sojojin kasar da ke fafatawa a fagen-daga.
Shi ma gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da ke tare da Tinubu a fadar ta Shehun Borno ya yaba da ci gaban da aka samu ta fuskar kulla alaka tsakanin hukumomin tsaro da gwamnatin jihar.
Mun ga alakar kut-da-kut da aka kulla tsakanin jiharmu da hukumomin tsaro. Hakan ya haifar da sakamako mai kyau. Za mu ci gaba da himmantuwa don cimma manufar yaki da matsalar tsaro a ko’ina a Najeriya. Inji Zulum.