Labarai

Muna Bukatar a Gaggauta Bincike akan Harin Bom da Sojoji suka yi wa Masu Maulidi – Kungiyar Agaji

Kungiyar agaji ta munazzamatu fitiyanul Islam reshen babban birnin tarayya Abuja

Tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta jgaggauta bincike da hukunta duk wanda yake da hannu a wannan mummunar aika aika na jefa bom a gurin Taron Maulidi a Garin tundun faira a jihar Kaduna

A Wata Sanarwa da Kungiyar ta fitar ta Hannu Mukaddaahin Jami’in Watsa Labarai na Kungiyar Muhammad Sani Yusuf Kungiyar Agajin ta Kara da Cewa lallai baza a lamunci kashe mutane kamar kiyashiba sannan Hukuma bata yi wani abu akai ba

Muna Bukatar a Gaggauta Bincike akan Harin Bom da Sojoji suka yi wa Masu Maulidi - Kungiyar Agaji
Muna Bukatar a Gaggauta Bincike akan Harin Bom da Sojoji suka yi wa Masu Maulidi – Kungiyar Agaji

baza muyi shiru ba da Bakinmu mu tsaya Muna kallon irin Wannan cin Kashin da Jamian Tsaro ke Yiwa rayukan Al’umma ba, adon haka Lallai Muna Kara kira a gaggauta kafa kwamitin bincike Don Gano Hakikanin abinda ya faru da kuma Tabbatar da an hukunta wadanda suka Aikata wannan aika aikar

Sannan ya zama Wajibi a biya diyyar mutanen da suka ras Rayukansu sannan wadanda suka jikkata a Basu kyakkyawar kulawa Domin ganin sun Samun lafiya

Daga Karshe Wannan kungiya ta Agajin Munazzamatu Fityanul Islam na Sakon sakon Ta’aziyya ga yan uwa da abokan arziki ga wadanda lamarin ya shafa sannan muna yi musu addu’a tare da fatan Allah ya Kiyaye faruwar irin Wannan anan Gaba.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button