Labarai

DA SAURAN RINA A KABA; Majalissar Kano ta watsa wa Ganduje kasa A ido, Taki Aminta Da sake Nada Sarakuna 4 A Kano

Majalissar dokokin jihar Kano taki amincewa da yiwa dokar mayar da Sarakuna 4 da gwamnatin ta kirkira a baya zama na 2.

‘Yan Majalissar sunki amincewa da sabuwar dokar karin sarakunan bayan daukar sa’o’i suna tafka muhawara a ranar Laraba, kamar yadda Gidan Radion DAFO FM ya Nakalto.

Tin dai a ranar 21 ga watan Nuwambar 2019 wata babbar Kotu a jihar Kano ta ruguje sabbin nadin da gwamnatin jihar tayi.

Majiyoyi daga zauren Majalissar ta shaidawa KANO FOCUS cewa; “Dayawa daga cikin ‘yan Majalissar jihar ta Kano basu gamsu da yacce ake tafiyar da yin dokar ba.”

Inda suka tabbatar da cewa ‘yan Majalissar sun bukaci da abi dukkanin wani tsarin dokar a kuma bi a sannu tare da jin da bakin al’umma jihar Kano kafin a aiwatar da dokar domin gujewa tashin hankali kamar wanda yaso faruwa a baya.

Majiyoyin sun sake tabbatar da cewa; Yan majalissar sunki aminta da yiwa dokar karatu na biyu bisa yacce gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje, ya bawa kanshi cikakken iko wajen yin dokar wanda hakan zai bashi damar; Zaben masu nadin Sarkin (King Makers) da kuma yin uwa da makarbiya wajen yiwa Majalissun Kasafin kudade.

Haka zalika daga cikin yan Majalissar da suka yi wa zaman dokar bore sunki amincewa da tsarin dokar data haramtawa kowanne Sarki baiwa gwamna shawara har sai gwamnan da kanshi ya bukaci hakan daga Sarakunan.

Sun bayyana haka a matsayin wani shiri na tauyewa Sarakuna hakkin da kasa ta basu na fadar albarkacin bakinsu.

Zuwa yanzu Majalissar ta dage zamanta zuwa gobe Alhamis domin cigaba da tafka muhawara akan yiwuwar yi wa dokar karatu na 2.

Me zaku ce?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button