Ƴan bindiga sun ƙona mata da sirikarta da yara biyu a Sakkwato
Wasu ƴan bindiga sun kona wata mata tare da da sirikarta da kuma ‘ya’yanta biyu da ransu a wani harin da suka kai a garin Sakkwato.
Daily Nigerian ta rawaito cewa an ce ƴan bindigar sun kai harin ne a kauyen Kurya da ke karamar hukumar Rabah a jihar da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutanen kauyen 12 tare da sace mata uku.
Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce daya daga cikin wadanda aka sace ta rasa mijinta a harin.


“Daga cikin wadanda aka kashe akwai wata mace daya da aka kona ta mutu tare da surukarta da ‘ya’yanta biyu a cikin dakinsu,” in ji shi.
A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani kazamin fada da sojoji.
“Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga jini a inda suka ajiye babura. Amma kun san ba sa barin gawarwakinsu a baya,” inji shi.
Sai dai rundunar ƴan sanda a jihar ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai yayin harin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i, ya kara da cewa suna ci gaba da
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






