Hotuna: Famfon ban ruwan noman rani, da ke amfani da batiri mai aiki da hasken rana – Dr. Hadi Usman
Dr.hadi usman dattijo mai kimiya da fasaha wajen kirkira wanda yayi fice a nijeriya, babba dr. hadi usman mutum ne mazauni gombe wanda ya fara kirekire tun shekarar 1970 wanda ya kirkiri rediyo wanda ya kewa duk jihar gombe.
A cikin hirar da Bbchausa nayi da shi ya fadi cewa a lokacin yayi wani abu wanda kamar wayar salula domin a lokacin ba’a san waya ba. Wanda ya haɗawa mutane tare da suke amfani wajen kiran matarka idan baka gida, amma duk sun mayar sai mutum daya kacal ne bai mayar ba.
Wanda kowane cewa yake wannan tsafi ne wata aljana ce ya sanya tana murya matar mutum.
Bugu da kari dr. Hadi usman ya kirkiri jirgi mai mazauni biyu wanda sun tashi sun kewaya a jihar gombe amma daga karshe sunka fado akan ba’a san yadda za’a sauko kasa ba.
Watan da ya shude jami’ar gombe ta karama hadi usman da muƙamin Dr duk da bai taɓa shiga aji ba wanda labarin ya kara de duniya.
To yau kuma Dr hadi usman yazo wa al’umma manoma rani wani cigaba da zasu futa da sayen man fetur inda tabbas wannan babban cigaba ne, yanzu kuma ga wani ci-gaba.
Mun gwada karamin famfo na ban ruwa na noman rani kuma yayi aiki yadda muke so, domin samun sauki wajen ban ruwa ga noman rani battery ne yake jawo ruwan wanda shikuma battery din yakan samu chaji ne daga hasken rana, mun samu sauki wajen sayan man fetur domin aiki da inji kuma babban sa yana nan tafe.
Ga hotunan nan.