Labarai

Gwamnan Zamfara ya raba wa sarakunan gargajiya motoci 260

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya saya wa sarakunan gargajiya motoci 260 a jihar.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar lll ne ya kaddamar da tutocin motocin a jiya Laraba a Gusau, babban birnin jihar

Motocin sun haɗa da sabon samfurin Cadillac 2019 don Sarakuna 17, Manyan Hakimai 13 da Hakimai 230.

Gwamnan Zamfara ya raba wa sarakunan gargajiya motoci 260
Gwamnan Zamfara ya raba wa sarakunan gargajiya motoci 260

Daily Nigerian hausa ta ruwaito cewa da yake jawabi a wajen taron, Matawalle, ya ce sun yi hakan ne domin ganin irin rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Kamar yadda mu ka sani, rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen samar da hadin kan kasa, kare martabar mu, da kuma zama abin koyi ga al’ummarmu, ba zai musaltu ba.

“A matsayinsu na shugabanni na farko a cikin al’ummominmu, sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen magance rikice-rikice da kuma taimakawa gwamnati wajen ba da shawarwari irin na iyaye ga talakawansu domin samar da zaman lafiya da juna,”

Tun da fari, a nashi jawabin, Sultan ɗin ya yaba wa Gwamna Matawalle a bisa wannan kyauta da ya yi, ya kuma yi kira ga waɗanda su ka amfana da motocin da su ci gaba da riƙe mutuncinsu da girman su a matsayin iyayen al’umma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button