Kwaɗayi ko yaudara: An fasa aure saboda ƙarancin lefe da ango yakai
Wannan wane irin abu ne duk irin tsada rayuwa da ake amma ace wai saboda lefen an fasa aure, abunda al’ada ne baya cikin addinin musulunci.
Wannan wani matashi ne da ake amfani da manhajar X @Musbey ya wallafa cewa abokin su ya kai lefe akwati biyar amma an fasa aure saboda sun rena nemansa.
Abokina ya kai lefe akwati biyar an dawo masa dashi, wai yayi kadan. Bikin next month ne on 12 January 2024.
— MUSBEY. (@zaMusbeyNe_) December 26, 2023


“Abokina ya kai lefe akwati biyar an dawo masa dashi, wai yayi kadan. Bikin next month ne on 12 January 2024“
Ya kara da cewa :
Yace min N2.7million ya kashe a duka akwatin. Gaskiya basu kyauta masa ba.
— MUSBEY. (@zaMusbeyNe_) December 26, 2023
“Yace min N2.7million ya kashe a duka akwatin. Gaskiya basu kyauta masa ba”
Wannan maganar ta jawo cece kuce sosai a kafar sada zumunta inda mutane sunka tofa albarkacin bakinsu.
@Idris_abdul_ahmed cewa yake:
2.7 million suka rains? Omo.. in har ya aureta be cika Dan halak ba. And yarinyar batasonsa tunda har ta bari aka dawo da akwatin
In nine babansa, wallahi aure zan hada dashi da wata yar family a ranar.
@frontier cewa yake :
In nine shi zan fasa musamman in ban yiwa iyayenta wani taklifi ba.
Waɗannan bid’o’in suna nema su durƙusar da al’umma.
@maxajee cewa yake :
Ya kamata mutane su san cewa wace zasu je neman aure.
Baze yu kaje ka haikewa grade din yan akwati 12 ba bayan kasan capacity dinka be kaiba.
Kowa da level dinsa shine ya debo da zafi. Ya tattara kayansa yayi hayin malam bello, akwati 3 zaa karba cikin karamci.
@yarimaahmed cewa yake :
Lallai fa Allah ya rufa asiri
Hope dai ba daga labarina sukayi copying ba kasan yanzu wayensu abunda ke faruwa wlhy daga film suke koyowa .
@Aminaaa cewa take yi :
Sual: Shin ya samu wata yanda baza’a canza date din ba? Ko har yanzu yana tunanin zasu canza ra’ayinsu?.
@Farukhalilu cewa yake yi :
In fa ɓera da sata, daddawa ma da wari. Bazai yiyu iyayen yarinya su tiƙe su cika ma gida fam da furnitures sannan ka kawo musu kaya kashamo-kashamo ba.
Akwai adalci kai akwatin 500k gidan da zasu ma furniture ɗin 5m? Ƙwarya tabi ƙwarya.
@Mansour cewa yake : Malam albarkar aure ake nema ba kayan daki ba ko kayan lefe ko baka taba ganin inda iyayen mata suka dauki nauyin aure ba hadda gida suke providing saboda basu dauki rayuwar duniya wani abu ba. Duk yadda zaayi fa sai wani side yafi kashe kudi perfection belongs to Allah alone.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




