Kidaya challenge: Rarara kaji tsoron Allah – Abis fulani
Shahararren mai amfani da kafar manhajar titkok Abubakar sadauki wanda ankafi sani da abis fulani wanda yake kokari wajen yin bidiyon domin wayar da kan al’umma da basu labarai da dumi duminsu.
Abubakar sadauki dan Najeriya ne wanda ya tafiya karatun digiri na biyu “Master’s” a kasar jamus “Germany” karatun lissafi da yake Allah yayiwa wannan matashi baiwa a fagen lissafi domin a karatun digiri dinsa ya fito da sakamakon farko a ajinsu “First class” Kenan, shima ya fito ya yi nashi sako ga fitaccen mawakin nan dauda kahutu rarara akan gasar kidaya da yake son matasan arewa suyi.
Abis fulani yayi magana sosai akan muhimmancin kidaya da kuma rashin kyautawar rarara akan gasar a yanayin da ake ciki a arewacin najeriya ga abinda yake cewa:
“Kidaya abu ne mai muhimmanci sosai nayi maganar sa kafin a daga shi kuma babu wanda ya bani ko sisi nayi wannan bidiyo a baya , to yanzu ma zanyi bidiyo na magana daban akanshi Rarara wallahi billahi azim kaji tsoron Allah, dan Allah dan annabi ka dunga saka tunanin mutanen arewa kafin kayi wani abun lokacin siyasa ya wuce.
“Yanzu ya kamata kayi abinda yan uwanmu da mutanen zasu cigaba fisabilillahi ana tsaka da kashe kashe mutane ana sace yan uwanmu da iyayen a daji amma babu abinda ka saka muna sai da yiwa tinubu waka wai baba tinubu yan arewa na godiya da kake nunawa duk abinda ya shafi yan arewa baya gabanka, inda ba abin neman kuɗi bane.
“Abis fulani ya kara da cewa da farko baka taba waka ka nunawa shuwagabanni nan matsalolin da arewa ke fuskanta ba.
Bugu da kari ba’a dade da munkayi kamfin din arewa mufarka ba manya sananu “celebrities” irinsu Ali Nuhu sunka fito sunkayi magana amma kai ƙus baka ce komai ba, saboda kana tsoron kayi magana suki baka aikin waka nan gaba.”- inji abis fulani
A aje wannan magana gefe.
“Yanzu gasa ta fito ɓurum ka fito kayi magana sananu “celebrities” irin su Ali nuhu sun fito sunyi magana amma miyasa kai baka taɓa magana ba, ni ban sani ba ko nine kawai nake da wannan tunani ba, yanzu su yan kudu korafi suke akan kasafin Kuɗi na kidaya ma sunyi yawa ina kira ga dauda kahutu rarara da wallahi kaji tsoron Allah”.-inji shi abis fulani.
Abis yayi maganganu masu ma’ana sosai a cikin wannan bidiyo da ya wallafa a shafin na tiktok @abisfulani.
Ga bidiyon nan ku saurare da sauran bayyani.
@abis_fulani Arewa Mu Farka…. #abis_fulani #securethenorth #arewapeople #nigeria ♬ original sound – Abubakar sadauki????????