Labarai

Catalonia ya amince da shirin ballewa daga Spain

Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya ce, yankin ya amince da shirin ballewa daga kasar Spain bayan kashi 90 cikin 100 na masu kada kuri’a a zaben raba gardama sun goyi bayan matakin ballewar.
Shi dai Carles Puigdemont na bayyana wannan matsayi ne bayan an kwashe jiya ana arangama tsakanin masu goyan bayan shirin zaben raba gardamar da jami’an tsaro.
Jordi Turull mai magana da yawun gwamnati ya ce, mutane sama da miliyan 2 suka kada kuri’a wanda ya kai sama da kashi 42 na masu zabe a yankin.
Akalla mutane 92 suka samu raunuka daga cikin mutane 844 da suka bukaci kulawar likita, yayin da hukumomin yankin suka ce, ‘yan sanda 33 suka jikkata.
Tashin hankalin ya dada zafafa tankiyar da ake ciki a kasashen waje da kuma tsakanin gwamnatin Firaminista Mariano Rajoy da na yankin Catalonia.
Rajoy wanda ya bayyana zaben a matsayin haramtacce ya ce, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile shi duk da arangamar da aka yi ta samu.
Kungiyoyin kwadago da masu zaman kansu sun kira yajin aikin gama-gari daga gobe Talata saboda abin da suka kira take musu hakkokin su.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button