Labarai

Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba,Eh ya fada siyasa!!!

Wanan shine rubutun wani ustaz wanda ya yi rubutu da ake mamakin yinsa wanda zakuji irin yadda yayi kalamai cikin hikima sosai.

Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba. Eh ya fada siyasa!!
Sheikh pantami, Femi Fani kayode, Dr bello Matawale

Wannan shine karo na farko da zan bayyana malam Sheikh Isa Pantami da kalmar dan siyasa, babu shakka malam ya jefa kafarsa a harkar siyasa babu wani boye-boye, kuma kin yarda da haka rainawa kanka wayo ne!.
Bawai shigar malam siyasa bane abun aibu, aa wallahi, naso ya shiga ayi dashi Allah ya bashi sa’a ya rike masa a duk makamin dayake so.
Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba. Eh ya fada siyasa!!
Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba. Eh ya fada siyasa!!

Amma inda raina ya bace malam ya bayyana siyasar sa, ta hanyar da duk wani masoyinsa sanda ransa ya bace, wajen gaiyato kafiri, mai bayyana kiyayyar sa ga Shehun mu Usman Dan Fodiyo dama addinin musulunci da yankin mu na arewa, kuma wannan kafirin da malam ya gaiyato ya taba cin mutuncin sa shi malam din, ta hanyar jefashi da dan ta’adda, wanda ya jefa bakin ciki a cikin ilahirin masoya malam din, wanda a lokacin munyi tayi masa raddi babu iyaka…
Amma kwatsam sai mu wayi gari muji malam ya gaiyato wannan mutum zuwa gidansa cin abunci, kawai domin wannan mutumin ya canja dheka zuwa jam’iyyar ubangidan malam, wato Buhari, sai malam ya gaiyato shi ya domin nuna masa farin cikinsa da shigowar sa jam’iyyar su.
Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba. Eh ya fada siyasa!!
Tabbas idan yau ka kira Prof Isa Pantami da dan siyasa, bakayi laifi ba. Eh ya fada siyasa!!

Naga wasu masoya APC suna son su raina mana hankali, ta hanyar kwatanta abunda malam Pantami yayi da kuma abunda Annabi yayi da kafiran makka, ko Da’ifa wannan jahilci ne da son zuciya, kwarai kuwa.
Da da’awa malam yake son yi masa, mai kama data annabta, da zai gaiyato shine tun lokacin da yake tsitstsille shi ta hanyar zagi da la’anta, tare da zama dashi domin janyo hankalin sa akan abunda yakeyi ba dai dai ba, kuma wallahi a lokacin idan ya gaiya ce shi ko ya taka yaje wajensa zai saurare shi babu shakka kuwa.
Amma ko kunsan idan a lokacin ne malam yayi irin wannan abu kujerar sa zatayi rawa? Wallahi kujerar sa bazata daure ba, zasu tunbuke shi.
Dan haka babu wata maganar addini anan siyasa ce kawai tsagoranta, ku daina kwatanta annabi da ire-iren wadan nan aiyuka domin rufe karya da lullube ta…
Ku sani ba siyasar malam nake kyama ba, ina ma so idan ya fita takara zanma yi masa kamfen a facebook, dan haka yanzu idan akayi ma Pantami suka ta irin siyasa mu daina jinginata ga addini, sai randa aka taba akidar shi.
Wannan shine….
Muhammad Ismail Ali.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button