Auren Mutumci tare da neman albarkar allah a cikinsa auren yar jarumi Ahmad gidan dabino


A wannan zamani da muke ciki, anriga ammaida aure kamar wata al’ada ba ibada ba, aure ya zama gasa yadda wasu ke yinsa kawai saboda abokai ko kawaye sunyi, dan haka su ma suke ga ya kamata su yi.
Mutane basa daukar aure da daraja da mutumci a wannan zamanin, yadda za kaga ana bidi’oi marasa kyau da ka iya sa Allah ya kwashe albarkar da ke cikin auren ya bar ma auratan da halinsu.
Da yawa mutane suna mamakin yadda za su ga anyi Soyayya tsakanin mace da na miji kai kace idan akai auren ko tari daya in ya yi dayan ma sai ya yi, saboda shakuwa da suka yi kafin a yi auren.
Tabbas akwai so da kauna mai karfi a tsakaninsu. To sai dai a ina gizo yake sakar ne da za kaga da anyi aure a wanna zamanin da ya lalace?


Na taba jin wata lacca da Dr. Muhd Sani Umar R/lemo ya yi akan abinda ke ruguza auren wannan zamanin.
Yawancin abinda ya fada ba shi muke gani ya ke kawo sanadiyar rabuwar auren ba. Wannan bidi’oin na zuwa “Party” ko “Dinnar”. da irin ta’sar da akeyi idan anje, shine ummul-abaisun da yake janyo aure ya lalace. Yace Hudubar auren da aka yi shi da al’adun banza da wanda aka yi shi bisa koyarwar Islama, duk daya ce.
Kawai ana samun matsala ne bayan da aka shirya fitsara da kuma aikata abubuwa da sunan wayewa, da ka iya janyowa Allah ya zare albarka a cikkn auren.


Saboda haka, da anyi aure an watse an tare sai kai ta ganin fitittinu na ta fitowa ko ta wanne bangaren har sai auren na ya ruguje.
Duk wanna bayanin nawa, na yi shi ne game da AUREN babbar yar Ado Ahmad Gidan Dabino wato Fati. Jiya aka daura auren a Masallacin Alfurqan karkashin jagorancin Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar.


Abunda zai burge ka malam shine, babu wata bidia irin wacce muka saba gani a sauran bukukuwa da aka yi a wannan aure. Kai hatta kida da mata kanyi acikin gida su dan rausaya, ba’ayi a wannan aure ba.
Da yake ita wannan amaryar yar albarka ta gama haddace Alqura’ni gaba dayansa a kanta( ba wai sauka ba, domin sauka daban hadda daban)
Sai ta tara kawayenta da sauran yan mata yayan gidan mutumci, inda suka zauna suka yi saukar Alqur’ani mai tsarki a tsakaninsu.
Babu shigar banza babu raye-raye da kade-kade na auren wannan zamani.
Wannan abu ya burge mutane da dama musamman duba da cewa mahaifin Amaryar fitaccen Jarimi ne a cikin Shirin Kwana Casa’in, na Arewa24, wato Malam Adamu da ke fitowa a matsayin Gwamnan Garin Alfawa.
Ina adduar Allah yasa sauran yan mata da samari da ba su yi aure ba, za su yi koyi da wannan aure, Allah ya sanya albarkarsa, yasa mutuwa ce kadai zata raba shi cikin ikon Allah.
Ameen ameen.
Rubutawa : Hassan Auwalu Muhammad