Kannywood

An Zabi Hamisu Breaker A Matsayin Gwarzon Mawaki Na Shekarar 2020

Advertisment
Fitaccen mawakin nan wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya lashe gasar zama fitaccen mawaki na shekarar 2020
Jaridar Online ta Amintacciya ce ta shirya gasar inda ta nemo mawaka guda 10 a cikin su Hamisu Breaker yai nasara.
Yadda akai zaben shine jaridar ta fitar da cewa zatai zaben ne ta hanyar sanya hotunan mawakan duk wanda yafi samu wadanda sukai like da hoton sa shi zaiyi nasara.
Cikin mawaka guda 10 Hamisu Breaker shine wanda yafi samun wadanda sukai like da hoton nashi sakamakon nuna shaawar wakokin sa da mabiyan shafin sukai.
Jaridar ta Amintacciya ta fitar dashi a matsayin Gwarzon Mawakan ta a 2020 inda ta bayyana cewa ba ita tai zaben ba, mabiyan ta ne, ita kuma Amintacciya tana alfahari da mabiyan ta duk wanda aka zaba shine nata.
A karshe wannan Jarida tana taya fitaccen mawaki Hamisu Breaker Murnar samun wannan Nasara daga Mabiyan ta.
Kuma tayi alakawarin bashi takardar shaidar wannan gasa anan gaba,kamar yadda arewablog na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button