Kannywood

Kiris ya rage nayi wuff da khadija Malumfashi – Ayyatullah tage

Jarumin fina finan barkwancin, ya kuma shaida cewa yana da kyakkyawar alaka da jarumar tun kafin ta fara fina finan Hausa.

Har ilayau Ayatullahi Tage ya kalubalanci ‘yan matan dake cigaba da fitowa suna sukar masana’antar Kannywood da sunan cewa suma daga cikinta suke, yace daga ganin irin wadannan ‘yan mata ko baiwa ta zama jarumai basu da ita.

Kiris ya rage nayi wuff da khadija Malumfashi - Ayyatullah tage
Kiris ya rage nayi wuff da khadija Malumfashi – Ayyatullah tage

Ayatullahi Tage ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Nishadi@360 na Kanawa Radio wanda ake gabatarwa duk ranar Asabar 7:00pm na dare.

Ayyatullah tage yayi kira da mutane su zamo masu kirki domin kuwa a duk lokacin da ka mutu za’a fara dauko ayyukan ka shin wane mutum ne mai hakuri ko mai yafiya,to yana da kyau mutum yazamo mai yafi da hakuri da juna, jarumi yayi wanannan kiran ne domin jimamin mutuwar darakta aminu s bono.

“Ita Khadijah Malumfashi tun a farko soyayya munka fari yi da ita, saboda wasu dalilai da na hango kada nace na aure ta su zo su faru shiyasa kawai,mua nan sai kawai ta cemin zatayi fim, wanda tun lokacin da muke soyayya da ita ba ta fim tana karama ce.

Saboda mun dade tare da ita wanda da ace abinda dan adam yake so a zuciyarsa alkhairi da naso na aure ta tuni, dalilinsa da yasa na fara aurenta shine.

Abu na farko idan maza sun tashi aure basu duba irin daidai da su wandanda zasu aura, wanda idan ka duba mace mai kyau tace zata aureka a duk yadda kake, kai kuma sai ka fara tunani minene zaka samar mata a matsayin ka na miji, kuma kai a wane mataki kake.

Saboda a lokacin ban fara YouTube ba ina zuwa wajen fim ne muna dauka kamara ana bamu dubu biyu ukku wani lokacin kyauta ma zakayi, to idan ka auri mace mai kyau baka da hali a wani lokaci magana ma idan kayi mata bata saurarenka duk da akwai so da kauna -inji Ayyatullah tage.

Ga bidiyon nan ku saurari cikakkiyar hirar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button