Labarai

Shawara da tsokaci akan yadda kanwa ta zalunci Yar yayarta ta riko

Advertisment

Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, musamman Zamantakewar Aure, Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. A yau ma shafin na tafe da tattaunawa kan wani sako da ya ci karo da shi game da cin amana. Jaridar Leadership hausa ne ke ruwaito wannan labari.

Ga sakon: “Na yi tafiya na tsawon shekaru shida, na bar ‘Yata me shekaru takwas a wajen kanwata. Ina biya mata kudin makaranta tare da ‘ya’yan kanwar tawa guda biyu duk da cewa tana da aure. A kowanne wata nakan tura wa kanwata dubu saba’in na ciyarwa da sauran hidimomi, wani lokacin ma har dubu dari dan kawai na tabbatar da ‘Yata ba ta rasa komai ba, ita ma kanwata haka. Na bude wa kanwata wurin sana’a don kawai in tabbatar tana cikin walwala, saboda mu biyu ne kawai muka rage.

Haka nan na siya wa kaina filaye guda biyu, sai kuma wani fili mai girman gaske wanda na shirya gina gida biyu daban-daban, daya na kanwata daya kuma nawa, kamar dai gidan dangi. Yaran kanwata su ne manya, nakan kira waya ta hoton bidiyo mu yi magana da ‘Yata, wanda hakan ya ba ni damar gane cewa ‘Yata tana cikin wani hali. Ban sanar da su zan zo ba, don ina son in yi musu ba-zata, kawai na hau jirgi na taho Nijeriya. Kwatsam ina shiga gida sai na tarar da kanwata tana dukan ‘Yata da ‘belt’ wai saboda ta jira ruwan sama ya dauke kafin ta dawo gida.

Ni ban sani ba, ashe tuni kanwata da ‘ya’yanta sun mayar da yarinyata baiwarsu, suna saka ta duk wani aikin gida, har ta kai ta makaranta mai nisa kuma me arha, duk da irin kudaden makarantar da nake turawa, ‘Yata ba ta cin abinci mai kyau, duk kayan da na turo mata masu kyau kanwata ta kulle su a akwati tana bai wa ‘Yarta ta saka, ya yin da ‘Yata kuma take saka tsumma. Duk kudin da nake tura wa kanwata don kar na wahalar da ita amma sau daya take ba ta abinci a rana, yanzu da na mutu kuma fa, wane irin riko za ta yi wa ‘yata? A gaskiya ina ji a raina cewa ba zan iya yafe wa kanwata ba.

Hatta mijinta ya sha yin fada a kan abubuwan da take yi amma ba ta ji. Yanzu haka ina tunanin hukuncin da ya dace na yanke a kan kanwata saboda kamar yadda na fada mu biyu kawai muka rage uwa daya uba daya a duniya? Idona ya rufe, amma don Allah jama’a ku taimake ni da shawara!”

Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannn batu, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:

Sunana Sadiya Garba (S.Girl) Jihar Kano:

Hmm.. Kaico an ci amanar zumunci, ai maganar yafiya ba ta taso ba, saboda ba ta duba zumunci ba ta ci Amana kuma ita ta aikata abubuwa da dama, wadanda Allah ya yi hani da su; Na farko ta ci amanar zumunci, na biyu tayi zambo cikin aminci, na uku an amince mata tayi ha’inci da sauransu. Kawai ta rabu da ita kunya ma ta isheta domin wallahi ko a haka ma ba za ta taba jin dadin rayuwarta ba sai ta tsangwami kanta, dama ai karshen zalunci nadama ne. Sannan dabi’ar manzon Allah (saw) ma ya yi Allah wadai da masu hali irin nata domin tayi zambo cikin aminci ne, dan haka masu irin wannan dabi’a ku ji tsoron Allah, ku sani azabar me cin Amana daban take musamman ma akan zumunci, duba da yadda ta aminta da ita Amma ta biye wa son zuciya da rudin shaidan ta aikata abin da zai zo ya zamar mata dana sani. Ya ubangiji Allah kayi mana tsari da cin Amana, da kuma sharrin zuciya.

Sunana Yakubu Bala Gwammaja:

Abin da zan yi mata shi ne; zan gaya mata abin da na gani, gaskiya idan na bar ta a raina zan dinga ganinta da abun a raina ba zan yafe mata ba, idan ni ne zan dauke ‘ya ta na bata kulawar da ya kamata ko nayi sauri nayi auren mace mai san yara. Na dan janye tallafin ga kanwata, ko hakan zai sa tayi hankali ta gyara.

Sunana Maryam Hussain Zariya:

Shawarata shi ne a yafe mata Allah yana san mai yafiya. A rage yi mata alkhairi saboda rowa babu kyau. Masu irin halin su ji tsoran Allah su san cewa kamatudinu Tudan.

Sunana Yahya Salisu:

A ganina a yafe mata tunda ‘yar uwa ce, a janye duk wani tallafi/gudunmawa da ake bata tunda ba ta da amana. duk mai irin wannan halin ya ji tsoron Allah ya daina domin har a wajen Allah laifi ne kuma cin amana ne.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button