Tabdi Jam: Dubun wani mutum ta cika da ke bi gidan mutuwa ya yi ikirarin yana bin mamaci bashi a biysahi


Wani mai suna Usman Yusuf Bala ya shaida cewa shi wannan mutumin aikinsa kawai shine bayan mamaci ya mutu sai ya bi diddigi yayi nazari game da wajen aikin mamacin da sauran kasuwancinsa sannan sai ya samu iyalan mamaci ya ce yana binsa bashi a biyashi.
Yanzu dai dubunsa ta cika an kamashi.


Ga abinda mutumin ke cewa
“Sunana Muhammadu sani kwana hudu nazo unguwa nan ne gaisuwa na manta sunansa nasan shi a kasuwa ba shi bane har ga Allah nazo nace ina binshi bashi amma ba hujja kuskure ne wannan
Ya kara da cewa har ga Allah ba halinsa bane rayuwa ce kawai bridgate kwana hudu yace shi asalinsa dan Maiduguri.”
Ga bidiyon nan ku kalla.
Mutane sunyi martani sosai akan wannan mutane inda wasu ke gasgata cewa tabbas wannan ba shi ne na farko ba kamar yadda zaku ga martanin mutane da dama.
@Ibrahim Abubakar Ustaz cewa yake : Ina ma mu muka kamashi da Wallahi sai mun gurfanar dashi a kotu sbd a iya labarin da samu akan wannan mutum karo na uku kenan da aka kamashi. Allah Ya ganar da masu hali irin nashi Ya shiryar dasu tare damu bakidaya.
@zaharadden musa yana cewa : Wlh yataba zuwa unguwarmu rasuwar mahaifin abokimmu yace yana binshi bashi huluna aka tamba yeshi wacce iriyar hula yace zanna bukar Al hali mutumin baya Saka hula zanna damanga sune hulunan dayake sakawa Kuma kowa yasan ba mutum bane maicin bashi domin kuwa Allah ya hore masa mukace abamu shi mu Zane shi manya suka Saka Baki aka kirawo yan sanda suka tafi dashi
@hamza Umar mechanical: Umar Mohammed Nasiru Allah Ya kyauta Amin.
Tabbas akwai wanda ya mana haka, kuma har yau sai da wani abu ya faru daga baya na tabbatar kawai ashe yayi amfani ne da lokacin da hankula ke tashe!
Abdulmalik Abubakar yana cewa : Subhanallahi wai Nigeria don Allah me yarage bamu Gani ba jama’a.
Dole mui tacin wuya a hannun azzalumai Allah ya tsare.