Labarai

Tinubu Ya Yabawa Dangote Akan Rage Farashin Dizal

Shugaba Bola Tinubu ya yabawa kamfanin Dangote Oil and Gas Limited bisa rage farashin man dizal.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai wato Ajuri Ngelale,da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ana amfani da mai na dizal mai yawa a Najeriya kama daga masana’antu da kamfanoni har zuwa motoci dake jigilar kayayyaki a fadin kasar.

Rage farashin man dizal daga baya zai shafi farashin kayayyaki ayyukan yau da kullum a fadin kasar tare da rage tashin gwauron zabi a kasar.

Kwanan nan Dangote ya sake duba farashin AGO daga Naira 1,650 zuwa Naira 1,000 kan kowace lita a kalla lita miliyan daya, tare da bayar da rangwamen kudi na Naira 30 kan kowace lita miliyan biyar zuwa sama.
Kakakin Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya na da kashi 20 cikin 100 na hannun jari a matatar Dangote.
Ya ce shugaban ya lura da muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jama’a da masu zaman kansu wajen ciyar da kasar gaba .

Mista Ngelale ya ce Shugaban kasar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ‘yan kasuwa da su sanya al’ummar kasar a kan abubuwan da suka fi muhimmanci tare da ba su tabbacin samar da yanayi mai kyau, aminci da tsaro don ci gaba.

Rahama Tv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button