Labarai

Har yanzu ina da burin auren G-Fresh – Jidda Babynice tsohuwar budurwar Kano State Material

Gidan rediyon Dala fm da ke birnin kano da ke arewacin Najeriya sunyi fira da Jidda Muhammad lawan wadda anka fi sani da Jidda babynice tsohuwar budurwa Al’ameen G-Fresh Kano state materials inda ta bayyana yadda sunkayi soyayya da irin yadda ta taimakesa a lokacinda baya tsamanin samun taimako daga wajen ta , duba da yayi aure kuma ba ita ya aura ba kishi kumallon mata bai sanya tayi kasa a gwaiwa ba lokacin da matarsa ta gaza agazamasa ita ce taje ta taimake sa.
Ga yadda firar ta kasance.

Har yanzu ina da burin auren G-Fresh - Jidda Babynice tsohuwar budurwar Kano State Material
Har yanzu ina da burin auren G-Fresh – Jidda Babynice tsohuwar budurwar Kano State Material Hoto/Dala Fm

“Ina matukar tausayin G Fresh Al’Amin a zuciya ta, kuma haka kawai naji ina tausayin sa.

Bazan taɓa mantawa dashi ba a rayuwa ta, domin munyi soyayya a baya Allah ne kawai yai ba Ni zai Aura ba, amma babu abinda yamin na tozarci.

Yanzu tsakani na dashi ya wuce soyayya ƙauna ce mai ƙarfi, kuma har yanzu ina da burin auren G-Fresh, idan Alkairi ne gare Ni ina fatan soyayyar mu ta dawo imba alkairi bane Allah ya zaɓa min abinda yafi alkairi.

“Jidda baby nice ta kara da cewa tace babban abinda yake burgeta da GFresh shine baya wasa da sallah a duk abinda yake idan lokacin sallah yayi zai tsaya yayi sallah.

Ta dalilin GFresh mutane suka sanni a duniya har yanzu idan ina tafiya a hanya ana fadin Babynice dan Allah nice babynice to kaga bazan taɓa mantawa da shi domin shine yasa anka sanni domin na dade ina Tiktok dina amma ba’a sanni ba, ta dalilin fara soyayya da shi duniya ta sanni followers dina sunkayi sama to alhamdulillahi bazan taba manta da GFresh ba ta wannan ɓangaren.”

Zaku iya sauraren fitar kai tsaye domin jin cikakken bayyanin firar da ankayi da Jidda Babynice.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button