Labarai
Kwankwaso ya samowa Dalibansa Gurbin Karatu a Jami’ar Mewer dake Kasar India
Advertisment
Daga Khadija Garba Sanusi
A yammacin yau ne Laraba 10/7/2019 Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kammala samarwa wasu daga Cikin Dalibai 370 yayan talakawa Gurbin karatu a Jami’ar MEWER UNIVERSITY dake Kasar India akan fannonin Daban-daban na ilimi Wanda Gidauniyar sa ta KWANKWASIYYA DEVELOPMENT FOUNDATION zata dauki nauyinsu zuwa kasashe daban-daban na Duniya.
zuwa yanzu dai Kwankwaso ya ziyarci Jami’o’i guda biyu akasar ta India a Cigaba da zagayen nemawa Daliban gurbin karatu da yakeyi akasashen Duniya a kakar karatu ta bana Wato (2019/2020 Academic Session).
Sanata Kwankwaso Yana tare da Rakiyar Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Kebbi Eng. Abubakar Sadiq Argungu.
Kwankwasiyya Reporters Nigeria
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com


![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






