Labarai

Gubar Illar da ke Cikin Shirin “Mata A yau” na Arewa24 tv – sheikh Kalimullah Ahmad Hinna

Advertisment

Qarfin zurfin tunanin wasu baya wuce iya abun da daqilewar qwaqwalen su ke kaisu cikin duhun Jahilci ba tare da sun sani ba. Wasu har inkari suke yi don shine iya maqurar ilimin su, wasu gani suke bai kamata ana magana akan su ba, wasu tsabar rashin sanin Addini da abun da ya qunsa, hakan da wadannan mutane ke yi da sunan MATA A YAU, ba laifi bane gare shi. Qoqarin yaqin qwalqwalwa wanda masu shirin Sabon Tsarin Duniya (New World Order) ke qoqari yi don tunzura mutane zuwa ga Ibadar Bin Zuciya, wanda wannan shine abun da suke haqqaqawa don tabbatar da ganin faruwar sa. Domin mun sansu bisa bayanin da Allah ya mana kan cewa:

ۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمْ عَن دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُوا ۚ

“Ba za su gushe ba suna yaqar ku, har sai sun muku ridda kubar Addinin ku qarfi da yaji, sai inda qarfin su ya qare”

Abun da galibi mutane suka jahilta kan wannar qadiyyar, galibinsu sun taqaita nazarin su kan abun dake kama da sunan wayewa alhali qauyanci ne dake kaiwa zuwa ga hallaka al’ummar musulmi cikin sauqi, a haka za a koma bautar raye rayen abun da zuciya ta quduri niyyar aikatawa sawa’un mai kyau ne ko marar kyau, ba tare da ganin girman illar dake ciki ba. Domin yaqi ne da suka kallafa kan dukkan wani mai Addini don tabbatar da abun da suke cewa “Greater Isreal” wanda kuma asalin sa so ake kowa yabar kowani irin Addini sai abunda suke so kowa ya aikata qarqashin ikonsu.

Wannan irin gurguwar tunani shine ya haifar da yawan sake saken aurataya tsakanin al’ummar musulmi, ga matan sunyi yawa, kuma idan sunyi aure ma basa zama. Domin sun dauki biyayya ga Miji a matsayin takura da matsi kan mace. Zawarawa sunyi yawa, ga budurwai basa auruwa, ko da sun auru cikin kashi Goma daqyar kashi daya ke iya jure zaman gidan miji. Suma a haka turawa kawai ake da sunan ana zaman aure, ba don komai ba, sai don anyi nisa da lamarin yanda Addini yace ayi, sai aka bi karantarwan yan Duniya don ya dace da irin shirin da suke so kowa ya koma kai.

Bari na fara mai furucin cewa wai idan mace bata gaishe da mijinta ba, wai sai shi ya gaishe ta, wannan ya sa6a da dabi’ar mu. Kuma aikata hakan raini ne. Ba laifi bane cikin Addini miji ya gaida matar sa, amma a irin inda muke rayuwa bamu saba ganin hakan ba, domin abun da muka sani tun asali shine, indai macen kirki ce ba zata qi fara gaishe da mijinta ba, balle har tayi tunanin jiran wai ya gaisheta. Babbar manufar masu tsarin Duniya kan masu irin wannan tunani yana neman cimma ruwa. Ga abunda suke son tabbatarwa:

“The New World Order will include changes in: the family: homosexual marriages will be legalized; parents will not be allowed to raise their children (the state will;.

Abun da suke shine kawo sauyi cikin rayuwar iyalai, da qoqarin qarfafar auren jinsi tsakanin maza yan Luwadi don a halatta yinsa (Wanda hakan shine abunda suke tallatawa kowace irin Kasa a Duniya). Qarshe abun da suke shine juyar da akalar tarbiyyar yara zuwa ga abun da suke son tabbatarwa.

Sai manufa ta gaba shine, bayan sun yi nasara kan wannan, daga anan za a dinga sakin aure ba kai ba gindi:

Furucin su na cewa dole ne mace tayi aikin Gwamnati ko dole mace ta fita tayi gogayya da maza wajen Kasuwanci. Abun da suke qoqarin isarwa shine, miji bai isa ya hana matar shi yin aikin gwamnati ba, kuma miji bai isa ya hana matarsa yin Kasuwanci ba ko da yana mata abun da ya sace na kyautatawar rayuwa. Manufar itace:

“All women will be employed by the state and not allowed to be “homemakers”;

Daga miji bayi da ikon hana matar shi fita wajen aiki, kuma bayi ikon sanin irin mutanen wurin. Daga cikin irin illar wannan aiki yake haifarwa shine qoqarin qirqirar alfasha. Shiya aure ba zai zauna ba, don ankai ta matsayin itama tana da iko da kanta.

Sakin aure zai zama ana yin shi babu kakkautawa cikin sauqi, kuma auren mace fiye da ďaya zai koma sai wane da wane, har a fitar wa mutane sha’awan yin aure. Zina tana sauqi, aure yana qara tsada. Ko anyi aure baya jiamawa, shine abun da suke so:

“Divorce will become ex- ceedingly easy and monogynous marriage will be slowly phased out”

Ga kuma asalin gundarin maganar tasu:

“The New World Order will include changes in: the family: homosexual marriages will be legalized; parents will not be allowed to raise their children (the state will;) all women will be employed by the state and not allowed to be “homemakers”; divorce will become ex- ceedingly easy and monogynous marriage will be slowly phased out”

Don haka, kai mai ganin bai dace ayi magana ba, watakila ka jahilci abun da baka sani ba, sai kake ganin hakan a matsayin shishshigi ne ko kuma tsoma baki ne cikin abun da mai shafe mu ba, alhali rayuwae Addini shine mafi ingancin rayuwa, kuma dole mu ankarar da mutanen irin illar da ake qoqarin haifar mush dashi. Babu daga saga cikim dake iya gina maganar shi kan Aya ko Hadisi, galibi suka magana ne irinta rayuwar wadabda ake so ace Na Miji da mace duk daya suke. Don haka, tana da haqqin aikata duk abun da take so.

Bana so na tsawwala, zan qara fitar da sharhin haka don mu qara fahimta a cikin rubutu na gaba.

Allah ya datar damu bisa hanyar dacewa

Rubutawa: Kalimullah Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button