Majalisa Ta Ce Sam Ba Za Ta Amince Da Bukatar Buhari Ba
Na Canja Sabuwar Dokar Zabe Kotu Kuma Ta Ce Dole Ne A Yi Abunda Buhari Yake So
Da alamu dai an samu rarrabuwar kawuna a ranar Talata kan kiran da majalisar dattawa ta yi na yin muhawara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na haramta sashe na 84 (12) na dokar zabe wanda dokar ta umurci duk wanda yake rike da mukamin siyasa dole ya a jiye mukamin shi zuwa karshen wannan na maris matukar zai tsaya takara a zaben shekarar 2023.
Rikicin dai ya faro ne a lokacin da Sanata George Sekibo daga jihar Ribas, yayin da yake dogaro da doka ta 10 da 11 na majalisar dattawa, inda ya tunawa takwarorinsa yadda ayyuka daban-daban na bangarorin gwamnati guda uku suke.
Ya kara da cewa hukuncin da kotun ta yanke, wanda ya soke matakin da Majalisar ta dauka, wani mummunan lamari ne da bai kamata a bari ya tafi haka ba.
Ya ce idan har aka bar batun, jam’iyyun siyasa za su iya kalubalantar matsayoyin majalisar a gaban Kotuna.
Sekibo ya bukaci takwarorinsa da su dakatar da sauran ayyukan majalisar na ranan domin zama tare da tafka muhawara kan batun.
Sai dai majalisar ta dattijai ta dage muhawarar kan lamarin zuwa ranar Laraba bayan ra’ayoyi mabanbanta kan wannan hukunci.
Me za ku ce game da wannan ta-taburzar da ake bugawa tsakanin Gwamnan Tarayya da majalisa?
Daga Comr Abba Sani Pantami