Labarai

Masarautar Idoma ta rage farashin sadakin aure saboda tsada rayuwa

Majalisar Sarakunan Gargajiya ta yankin Idoma a Jihar Benue ta soke wasu al’adu sannan ta yiwa wasu al’adunta kwaskwarima saboda tafiya dai-dai da zamani, majalisar ta soke shirya gagarumin bikin binne matattu sannan ta soke karbar haraji mai tsada kan iyalan wadanda suka mutu.

Wakiliya ta ruwaito Majalisar ta kuma rage farashin kudin sadakin aure, a inda ta kayyade Naira 50,000 a matsayin kudin sadakin aure a ƙasar Idoma,

Masarautar Idoma ta rage farashin sadakin aure saboda tsada rayuwa
Masarautar Idoma ta rage farashin sadakin aure saboda tsada rayuwa Hoto/facebook: Dclhausa

Babban mai rike da sarautar masarautar Idoma, Och’Idoma, Dokta John Elaigwu Odogbo, ya bayyana hakan a Otukpo, hedikwatar Idoma land yayin da yake isar da sakonsa na sabuwar shekara ga jama’arsa.

Och’Idoma, ya bayyana cewa an cimma matsayar ne bayan tattaunawa da sarakuna da shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a masarautar.

Ya kara da cewa, “duka sauye-sauyen a nan take za su fara aiki a kan dukkan kabilun Idoma, harsuna, da mutanen da ke karkashin masarautar Idoma”

Inda a yanzu mafi ƙarancin sadaki yafi dubu sittin 60k a kalandar I.E.T Sokoto amma saboda saukakawa maza wannan masarauta tayi, majalisar samari suna kira da al’umma duniya da suyi kori da masarautar idoma domin saukakawa marasa aure.

A wata ruwaya kuma dclhausa ta jiyo wani labari daga dailynisab.org cewa a halin yanzu Mafi karancin kudin sadaki a Nijeriya ya koma Naira dubu tamanin da shida da dari biyu da goma (N86,210.00).

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button