Labarai

Abubuwa biyar da Buhari ya gaya wa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar ranar Laraba kwana guda bayan ya nada su a kan mukamansu.
An yi ganawar ce a fadar shugaban kasar da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Bbchausa  ta ruwaito cewa a ranar Talata ne Shugaba Buhari nada sabbin manyan hafsoshin sojin kamar haka: Janar Leo Irabor, babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru – babban hafsan sojan ƙasa; Rear Admiral A.Z Gambo – babban hafsan sojan ruwa; da kuma Air-Vice Marshal I.O Amao – babban hafsan sojan sama.
Sun maye gurbin Janar Abayomi Olonisakin, Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar wadanda ya nada a 2015 bayan ya lashe zabe a karon farko.
 
Shugaba Buhari bai bayyana dalilin cire su ba amma ya dauki matakin ne lokacin da ‘yan Najeriya suka gaji da korafi a kansu suna zarginsu da gazawa wajen shawo kan matsalar tsaron kasar.
Sanarwar da Mr Femi Adesina, kakakin shugaban kasar ya aike wa manema labarai ta ce ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi ne ya jagoranci sabbin manyan jami’an tsaron zuwa wurin Shugaba Buhari wanda ya umarce su da su tashi tsaye wajen ganin sun magance matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya.
Ga abubuwa biyar da shugaban ya gaya wa sabbin hafsoshin tsaron na Najeriya:
Kishin kasa
Shugaba Buhari ya hori manyan hafsoshin tsaron da su kasance masu kishin kasa sannan su “bautawa kasa kamar yadda ya kamata” a yayin gudanar da ayyukansu.

Muna halin ta-baci

Shugaban na Najeriya ya shaida wa manyan jami’an tsaron cewa “muna cikin halin ta-baci” don haka sai sun zage dantse za su iya shawo kan matsalolin da suka yi wa kasar dabaibayi.
Ina taya ku murna
Shugaba Buhari ya taya manyan hafsoshin sojin murna bisa yadda suke jagorantar fannoninsu daban-daban, yana mai karawa da cewa “babu abin da zan gaya muku a kan aikin soji, saboda a cikinsa kuke. Ni ma da a cikinsa nake.”

Zan yi muku addu’a
Shugaban Najeriya ya ce zai yi musu addu’ar samun nasara tare da ba su goyon baya dari bisa dari.

“Ina ba ku tabbacin cewa zan yi duk abin da zan iya a matsayina na Babban Kwamandan Soji ta yadda mutane za su yaba muku,” in ji Buhari.
Ya kara da cewa “Kun san halin da muke ciki a 2015, kuma kun san matsayin da muke ciki a yanzu, da kuma alkawuran da muka dauka. Mun yi alkawarin wanzar da zaman lafiya a kasar nan, bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci. Dukkansu ba abu ne mai sauki ba, sai dai tabbas mun samu ci gaba.”
TikTok: Yadda shafin sada zumuntar ya zama matattarar samari da ƴan matan arewa
Anya Lampard zai iya sake samun babbar kungiyar da zai horar?
Adalci ga na kasa da ku
Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga sabbin manyan hafsoshin tsaron da su mayar da hankali wajen inganta rayuwar kananan soji, yana mai cewa ya kamata “su samu kwarin gwiwa a jikinsu da kuma aikinsu”.
Ya yi alwashin cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen samar musu kayan aiki da biya musu bukatunsu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button