Labarai

Kullum sai miji na ya duba al’aura ta idan na dawo daga aiki – Inji wata mata

Matar wani magidanci mai shekaru 42 a birnin Lusaka na kasar Zambia, ​​ta rabu da shi saboda kullum ta dawo da ga aiki, sai ya duba al’aurarta, bayan da makwabta suka gaya masa cewa ta na fita yawo da wani dan kasuwa.

A cewar jaridar Zambia Observer, matar, Bessie Msisika Chirwa, mai shekaru 39, ma’aikaciyar jinya ta kai Amos Chirwa, malamin makaranta, kotun Lusaka Boma, bisa dalilin cewa ya na duba al’aurarta a duk lokacin da ta dawo gida daga aiki, musamman da safe bayan ta yi aikin dare.

Su biyun sun haifi ‘ya’ya biyar tare bayan sun yi aure shekara 13 da wata 10.

An umurci Amos ya biya K600 duk wata don abinci da tufafin ’ya’yansu.

Amos ya yi kuka sosai a wajen kotu domin ba ya son ya rabu da kyakkyawar matarsa ​​wadda ya ce ya na matuƙar ƙauna.

(TRIBUNE)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button