Wata sabuwa : Wanda Ya Dauki Bidiyon Ganduje Zai Bayyana A Gaban Majalisa
Irin Sharrin Da Aka Yi Wa Nana Aisha Aka Yi Wa Ganduje – Dan Ci Da Ceto.
Daga Muzammil Mandawari
A daidai lokacin da wanda ya dauki video gwamna ganduje yayi ikirarin zai bayyana kansa a majalisa domin Kare kansa da bayyanar da gaskiyar abinda ya dauka
Wani murtaddi dan ci da ceto wanda yayi suna a zalinci Kala kala aka sha kamashi da danniya da babakere, amma dake sun raina addini wai shi a bangaren malanta yake, ya fito yana danganta wannan aikin da irin sharrin da akaiwa uwar muminai Assayida Aisha
Ba wai ina son na tabbatar da sahihanci ko rashin ingancin wannan videon bane A’a ina son na nusar da mutane yadda wasu bata gari suke shiga rigar malunta domin biyan bukatun su ba tare da tsoron Allah ba.
La shakka duk mai hankali ya san wannan maganar bata dace da fitowa ko daga bakin jahili ba balle mai ikirarin Malunta.
Allah Ka tsare mana imanin mu kada Ka bari son zuciya ya halakar damu.