Labarai

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da ƴar ta a Kano

Wani matashi ɗan shekara 20, mai suna Gaddafi Sagir, ya kashe kishiyar mahaifiyarsa mai suna Rabi da kuma yar ta, Munawwara a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a jiya Asabar da misalin ƙarfe 10 ma dare a unguwar Fadama da ke Rijiyar Zaki a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matashin na zargin marigayiya Rabi da yin sanadiyyar rabuwa da mahaifinsa, shi ne ya buga mata ƙarfe a wuya da goshi, nan take ta faɗi ta rasu da tsohon ciki a jikin ta.

Rundunar ƴan sanda a Kano, ta bakin kakakin ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka rundunar ta kama wanda ake zargin, inda ya ce a yayin binciken farko, ya amsa cewa shi ne ya kashe mamatan.

Ga bidiyon nan ku saurara kai tsaye hirar da kiyawa.

 

Gaddafi yace abinsa yasa sunyi fada da ita matar babansa inda yayi amfani da sukudire ba ya chaka mata a wuya shikenan ita kuma yar ta yayi amfani da dan kwalinta ua kasheta.

Wanda sufeton yan sanda kiyawa yace to miyasa ya aikata wannan aika aika yace saboda sun samu sabani da mahaifinsa dalilin haka yasa mamar tabar gidan wanda ita wannan margayi amarya ce bakinta shekara biyu da aurenta.

Suna ta fada da mahaifiyata suna fada na zage zage a gabana wanda har a gabana mahafina yana zagin mamar mu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button