Kannywood

Har yanzu ina kewar kalman soyayyar mu da Rahama sadau – Inji saurayin kurciya

Kafin Rahama sadau ta shiga film munyi soyayyar Free-call cikin dare har ku’din mashin nake bata a makaranta

Har yanzu ina kewar kalman  soyayyar mu da Rahama sadau - Inji saurayin kurciya
Har yanzu ina kewar kalman soyayyar mu da Rahama sadau – Inji saurayin kurciya

Na Sha Baiwa Rahama Sadau Kudin Babur Da Na ‘Yan Kananun Hidindimu, Amma Yanzu Ta Wuce Aji Na, Saboda Daukakar Da Allah Ya Yi Mata, Cewar Saurayinta Na Kuruciya

Saurayin Rahama Sadau tun ta kuruciya, Shu’aibu Abdullahi ya bayyana yadda soyayyarsu ta kaya a lokacin suna ajin SS2 a shekarar 2004 da jarumar.

A cewarsa, har kudin mashin da ‘yan kananun hidimomi yake mata, daga bisani kuma Allah bai nufa za su yi aure ba. Sannan kuma a yanzu ta wuce ajinsa saboda daukakar da Allah ya yi mata.

Ga bidiyon nan zaku saurari hirar daga bakinsa.

A wani labarin kuma Al Nassr Ta Sallame Shi Tare Da Ba Shi Milyoyin Kudade Domin Ronaldo Ya Maye Gurbinsa A Kungiyar

…idan kai ne za ka amince?

Kungiyar Al Nassr ta soke kwantiragin Vincent Aboubakar na Kamaru don maye gurbinsa da Cristiano Ronaldo.

A bisa ka’idojin gasar lig-lig ta kasar Saudiyya, kungiya na da damar daukar ‘yan wasan kasashen waje 8 kacal, kuma Al-Nassr na da adadin ‘yan wasan kasashen wajen, don haka ya zama dole dan wasa daya ya tafi domin Ronaldo ya samu gurbin buga mata kwallo.

Rahotanni na cewa an cimma yarjejeniya da Aboubakar kan ya karbi wasu kudade masu tsoka don ya janye wa Ronaldo.

Idan kai ne Aboubakar, me za ka yi?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button