Sheikh kabiru haruna gombe yayi magana akan karin kuÉin aikin hajji da ya zowa mutane kwatsam wanda a can baya ance miliyan HuÉu da dubu Éari shidda 4.6, a cikin tafsirinsa na jiya malam yayi magana inda yake cewa.
Alhazzai mutum dubu hamsin ne sunka biya ta kudin aikin hajji sai gashi Hukumar alhazzai tace sai kowa ya sake biyan naira miliyan 1 da dubu Éari tara , wani alhaji da kokuwa ya samu ya biya ya dauka ya kare wannan ajandar bai da komai yanzu ance sai ya kawo kusan miliyan biyu kafin yaje aiki hajji nan da kwana hudu.
Ga gwamnatin tarayya musulmi musulim, ga gwamnonin jahohi mafi yawan muslim muslim amma ba’a yiwa dakin Allah alfarma ba, Allah baza’a yi masa alfarma ba, wanda yake rayuwa a cikin wannan kasa don mi bakin ciki bazai kashe shi ba, dukiyar fa tamu ce, bata wasu bace, wannan fa addinin mune rukuni ne Daga cikin addinin mu.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce gwamnatocin Obasanjo da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari duk sun taÉa yi wa Alhazan Nijeriya cikon kuÉin Aikin Hajji domin samun sauĘi. Haka kuma ya yi kira ga gwamnonin jihohi su biya wa kowane maniyyaci na jiharsa cikon kuÉin da ya rage idan gwamnatin tarayya ta gaza biya.
A Tarihin aikin hajji a Nijeriya ba mu taba ganin irin wannan musibar ba.muna kara kira da ga mai girma shugaban kasa bola ahmad tinubu kayi amfani da gwamnatinka ta Muslim Muslim ka shafe wa addinin musulunci hawaye.
Sheikh Kabiru Gombe yayi maganganu da zaku saurara a cikin wannan faifain bidiyo domin suna da yawa.