Labarai

Atiku ya roƙi CBN ya ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi

Advertisment

Ɗan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga Babban Bankin Najeriya CBN da ya ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗin da aka sauya a ƙasar.

Atiku ya roƙi CBN ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi
Atiku ya roƙi CBN ya ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi

Cikin wani bidiyo da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce idan aka yi duba da halin matsi da al’umma ke ciki ya kamata a ƙara wa’adin zuwa wani ɗan lokaci.

A cewar Atiku sauya fasalin kuɗi ba wani sabon abu ba ne a fadin duniya, ka zalika matakin ba sabo ba ne ga Najeriya, sai dai wa’adin da aka tsayar na 31 ga watan Janairun da muke ciki na jefa mutane cikin mawuyacin hali.

“Da yawan ‘yan Najeriya musamman manoma da masu sana’ar hannu da mazauna ƙauyuka ba su da asusun banki, dan haka lokacin da aka ka’ide na daina karbar tsofaffin kuɗi ba mai yiwuwa ba ne,” in ji Atiku Abubakar.

‘Yan Najeriya da dama na ta kiraye-kirayen CBN ya sake nazari kan wannan wa’adi, la’akari da ƙarancin sabbin takardun kuɗin da ake da su a ƙasar.

 

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button