Labarai

Ya Daddatsa Mahaifinsa Da Adda Saboda Tayar Da Shi Daga Barci

Advertisment

Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani matashi da ake zargi da daddatsa mahaifinsa da adda, saboda ya tashe shi daga barci.

Ana zargin Ibrahim Sikiru mai kimanin shekara 27 da kashe mahaifin nasa, Mumini Ibrahim.

An kama shi ne bayan korafin da wani mai suna Abiodun Sunday, wanda makwancin mamacin ne ya shigar ofishin ’yan sanda na Onipanu.

Mutumin ya shaida wa ’yan sandan cewa wanda ake zargin wanda mai gadi ne ya dawo gida ne da safe inda ya tarar da dan nasa yana barci.

Advertisment

Daga nan ne ya tuhumi dan nasa a kan me yasa yake barci har zuwa lokacin.

Hakan ce ta sa ya fusata, daga nan kuma ya dauko adda ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa ’yan jarida ranar Asabar cewa jim kadan da samun rahoton ne ya sa suka aike da ma’aikatansu, inda suka kama shi.

Ya kuma ce sun garzaya da mahaifin da aka daddatsa zuwa asibiti, inda ya mutu a nan take.

Sai dai ya ce suna kyautata zaton wanda ake zargin matsafi ne, saboda ba shi da wani kwakkwaran dalili lokacin da suka titsiye shi a kan kisan.

Abimbola ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin mayar da wanda ake zargin Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar, don fadada bincike a kai.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button