Labarai

ƙasar Somalia, saurayi yana aure ne tsakanin shekara 17 – 18,In ya kai shekara 20 ba tare da ya yi aure kamasa za’a yi

Wani shahararren marubucin malam sukairaj Hafiz Imam ya kawo wannan labari wanda tabbas akwai ban mamaki sosai a cikin wannan rayuwar ta yan kasar Somalia wanda yan Nigeria suna mamakin irin wannan al’amarin ga labarin yadda yake.

A ƙasar Somalia, saurayi yana aure ne tsakanin shekara 17 – 18. In ya kai shekara 20 ba tare da ya yi aure ba toh a wannan lokacin dattijan ƙabilarsu zasu saka baki akansa domin zai jawo musu abin kunya da zagi a wajen sauran ƙabilu.

ƙasar Somalia, saurayi yana aure ne tsakanin shekara 17 - 18,In ya kai shekara 20 ba tare da ya yi aure kamasa za'a yi
ƙasar Somalia, saurayi yana aure ne tsakanin shekara 17 – 18,In ya kai shekara 20 ba tare da ya yi aure kamasa za’a yi

Saurayi a Somalia yana da ƴancin zaɓar matar farko ba tare da wani yace masa uffan ba.

Idan Matarsa ta yi haihuwar farko, toh Mahaifiyarsa zata zaɓa masa mata ta biyu.

A irin Al’ada ta ƙasar Somalia, mutum zaiyi murnar cikarsa shekara 30 ne da auren Mata ta 3.

Wajibi ne ya auri Mata ta 4 kafin ya kai shekara 40. Suna ganin ƙurewar abin kunya ne mutum ya kai shekara 40 bai auri Mata 4 ba.”

Martanin Mutane

@Anas Darazo cewa yake:

To Ya Sheikh me zai hana Arewa ma su koma haka? A tara hausawa a faɗawa kowa gaskiya.

@Sadiq Madabo : Garin daɗi na nesa

Amma yanzu gamu nan rusa-rusa, sai uban taurin kai. Ni ji nake kamar na wawwaskawa kaina mari ma

@Hauwy Muhammad : Allah yasa Mazan Nigerianmu, Suzuciya d jin wannan labarin Mai qawatarwa.

@muhammad sagir usman : Gaskiya zan koma Somalia Shaykh Sukairaj Hafiz Imam tunda a can an fi fahimtar darajar miji

@matukin Adaidaita sahu : Kut!
Gamu mun doshi 40 har yanzu muna lilo da guda biyu

@comared zaharadeen Yakubu : Garin Daɗi na nesa
Gamu nan mun Haure shekaru Arba’in ko tsayayyiya babu kuma idan Rayuwa taci gaba da tafiya a haka, zamu ‘iya Mutuwa babu auren.

Kowa ya san ni Comred ne

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button