Labarai

An Bayyana Sunayen Mutanen Da Ake Tuhuma Da Daukar Nauyin Yan Boko haram

A watan maris din daya gabata ne dai aka kama wasu mutane da ake tuhuma da laifin bawa yan bokoharam kudaden da suke gudanar da ayyukan su na ta’addanci wanda yayi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane.
A bayanin daya bayar, mai taimaka ma shugaban ƙasa a kafafen watsa labarai wato mal. Garba Shehu, ya bayyana cewa an kama wasu masu harkar canjin kuɗi wadanda sune ke taimakawa wajen shigo ma da ƴan ta’addan kuɗaɗe, jaridar Daiytrust ta wallafa.
Yace akwai wasu ƴan Nigeria dake turo ma ƴan ta’addan kuɗaɗe daga Dubai dake haɗaɗɗiyar daular larabawa ta hannun ƴan canjin waɗanda a hannunsu ne ƴan ta’addan na bokoharam ke karbar kuɗaɗen.
“Ƴan canjin sune ke taimakawa wajen shigo ma da ƴan ta’addan da kuɗaɗe. Akwai aikin haɗin gwuiwa da muke da hukumomin na Dubai. An samu nasarar kama ƴan Najeriyan dake aiko ma da ƴan ta’addan kuɗi. Haka nan ma anan gida muna nan muna ƙara gudanar da bincike wanda bayanan zasu yi matuƙar baiwa al’umma mamaki da zarar mun kammala.” cewar Garba Shehu.
Jaridar ta Dailytrust ta samu jerin sunayen wasu daga cikin mutanen da aka kama dangane da batun.
Akwai wasu ƴan kasuwar canji ta Wapa dake Fagge, jihar Kano waɗanda aka kama su a watan Maris da ya gabata. Daga cikinsu akwai:

  • Baba Usaini
  • Abubakar Yellow (Amfani)
  • Yusuf Ali Yusuf (Babangida)
  • Ibrahim Shani,
  • Auwal Fagge,
  • Muhammad Lawan Sani (wani mai hada-hadar cinikin zinare)

An bayyana cewa hudu daga cikin ƴan canjin da aka kama na da alaƙa da wasu mutum biyu da aka kama a Dubai a bara.
Dailytrust ta samu bayanan cewa haɗakar jami’an tsaro na DSS da DIA, Da NFIU da kuma babban bankin tarayya wato CBN ne suke gudanar da binciken.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button