Wasu Dalilan Dake Sa ‘Yan Mata Auren Tsofi
A darasin mu na baya mun kawo wasu dalilan dake sa ‘yan mata soyayya da tsoffin maza. Yanzu kuma mun binciko wasu dalilan dake sa mata masu karancin shekaru auren mazan da sukayi jika dasu.
Duk kuwa da binciken kimiya ya tabbatar da kwakwaluwan ‘ya mace yafi na danamiji budewa da saurin balaga. Wannan yana daya daga dalilan dayasa mata suke kin mu’amala da sa’anninsu. Ga wasu dalilan da suke sa wasu ‘yan matan auren dattijai.
1: Dattaku- Mata suna son mutum mai kamanta gaskiya. Mai magana guda. Wannan yana daga cikin dalilin da yasa ‘yan mata suke sha’awar auren dattijon namiji.
2: Gudun Yaudara: Shi dattijon mutum ba a sanshi da yaudara ba. Ganin akasarin dattawa suma sunada ‘ya’ya mata harma da jikoki. Yasa da wuyar gaske yayi alkawarin auren mace ya fasa. Mata kuwa musamman wacce aka taba yaudaranta ko aka yaudari wata na kusa da ita. Gudun yaudaran maza masu karancin shekaru yakan sa mata su gwammace auren dattajo mai cika alkawari.
3: Iya Lanlaba: Shi dattijon namiji yasan dabaru da hanyoyin da zaibi domin ya lanlabi mace a lokacinda ya bata mata ko aka bata mata ko kuwa ranta ya baci sabanin shi namiji mai karanci shekaru. Wanda hakan yasa mata suke son auren dattijan maza saboda hakan.
4: Hakuri Zama Da Mace: Yana daga dalilan dake janyo hankalin mata masu karancin shekaru auren dattijai. Su dattawa sunada gogewa wajen yadda zasu zauna da mace saboda jimawa da aure da kuma yawan mu’amala da mutane.
Shi dattijan namiji ba kamar namiji mai karanci shekaru bane wajen juriya da hakurin zama da mace. Wannan yasa kananan mata suka fi sha’awar su auri dattijo aurensu ya dore maimakon auren yaro ya kasa hakurin zaman aure dasu.
5: Abun Duniya: Akasarin dattawan dake sha’awan auren mata masu karancin shekaru masu rike da mukamaine ko masu saraura, ko manyan ‘yan kasuwa ko kuma manyan ‘yan siyasan da suna da abun duniya a jimge.
‘Yan mata sun gwammace su aure irin wadannan tsoffin su shiga daula maimakon auren saurayi suyi zaman talauci.
6: Kariya: Akwai matan dake auren dattawan maza wanda suke ma yin hidimar auren da kansu. Ko kuma iyayensu su aura musu su. Irin wannan auren wani lokaci anayinsa ne saboda samu mafaka da wani abun ki da yarinyar tayi a lokacinda take budurwa.
Akwai yaran mata da sukayi gagaran da suke rasa mazan aure, hakan yasa ko dai su dakansu su aurawa Kansu dattawan saboda karewa yawa ko kuma iyayensu su lakabawa wasu aminansu ko ‘yan aikinsu su aura domin a wuce wajen.
Mu fatanmu koma da yaya akayi auren, Allah Ya bada zaman lafiya da lafiyan da ma’aurata zasu iya gamsar da juna da samun zuriya mai albarka.
#Tsangayarmalamtonga