Labarai

Asalin abin da ya jawo cece kuce akan kalaman Hafsat Paki yar kaduna

Advertisment

Wata budurwa yar jihar kaduna mai suna hafsat paki tayi bidiyo a ciki take fadin makwabansu samarin garin kano basa yin bursh, basa yawan hawa mota ba turanci sosai a tattare da su.

Hafsat paki a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafin ta na sada zumunta Tiktok tana mai cewa:

“Wato makwaton mu kowa yasan su da Green shadda and yellow shadda da kaga haka mutum ne daga kano,basa zuwa makaranta amma suna da kokari kadan daga cikin su masu zuwa makaranta kan su na kawo wuta.

Asalin abin da ya  jawo cece kuce akan kalaman Hafsat Paki yar kaduna
Asalin abin da ya jawo cece kuce akan kalaman Hafsat Paki yar kaduna Hoto/X : hafsat paki

Basa yawan goge hakori “brush” ba karin waye wa dan kano zai ba kaga yana yin “brush” a koda yaushe suna dauka lokacin ko sai idan za’a je inda budurwa ana son a burgeta.

Sa’a nan idan ke ba yar kano bace kinkayi aure to kun kulla yarjejeniyar da shinkafa da wake a koda yaushe, watan da ya wuce munje kano nida yayata munka fara ƙirga mata masu tuki a kano, mata basa tuƙi a kano. Kadan daga cikin sune ke tuki kwana ukku da munkayi basu wuce mace ukku ba da mun ka gani.

Bayan haka munje wajen cin abinci “restaurant” ake kallon mu, mu cikakken yan iska ne munje “restaurant” cin abinci.

Hafsat paki ta kara da cewa shidai dan kano ko digiri ukku ne da shi PhD kenan turanci wala, basu fiye yin turanci ba,amma suna da kuɗi dan karamin yaro zaki ga ya dauke ki kunje “Super market” ya kashe miki ɗaruruwa Kuɗi sun da kudi kamar yan gidan mu yan kaduna ne basu saba da wannan ba. Bama sunda su balanta su yi, su yan kano gaskiya akwai kudin amma kuwa wanka zero, dresses zero exposure zero, amma suna da kuɗi – inji hafsat paki.

Ga son mace mai bleaching idan kin rasa kasuwa ko ina kiyi bleaching kije kano hannu daya zaki samu miji “one hand” Sa’a nan gidajen kaduna falo daya a kaduna zai iya yin two bedroom flat kamar guda ukku a kano, amma wasa nake yi.-inji hafsat paki.

Ga bidiyon nan ku saurara.

@hafsatpakiKano people hello

♬ original sound – The king herself

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button