AddiniLabarai

Ina neman afuwar tarin mazajen da na kasa a wurin nema auren amaryata, Sheikh Daurawa

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bai wa mazajen da su ka yi gasar auren matarsa, Haula’u hakuri bayan ya kasa su. Shafin Labarunhausa na wallafa

A wani sabon bidiyo wanda Freedom Radio da ke Kano ta saki a YouTube, malamin ya bayyana cike da farinciki yana bayar da hakurin.

Ga dukkan alamu an dauki bidiyon ne bayan an daura aurensa da zukekiyar amaryarsa, a cikin masallacin ne ya amshi abin magana inda ya ke bayar da hakurin.

https://www.labarunhausa.com/18062/ina-neman-afuwar-tarin-mazajen-da-na-kasa-a-wurin-nema-auren-amaryata-sheikh-daurawa/
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Angon Hafiza

A cewarsa, gasa ce aka shiga ta aure, kuma kowa ya san malami zai hada da addu’o’i idan zai shiga ko wacce gasa, watakil hakan ne yasa ya samu nasara.

Bidiyon wanda gajere ne ya tabbatar da rahoton da Labarun Hausa ta saki a kwanaki kadan da su ka gabata, wanda aka bayyana yadda malam yaje a matsayin Late Comer yayi wuff da zukekiyar budurwar.

Malama Haula’u asalin ‘yar jihar Kano ce, kuma mahaddaciyar Al’Qur’ani ce don ta lashe mukabakar Al’Qur’anin da aka yi na wannan shekarar.

Duk da dai mace ce mai karancin shekaru, majiyoyi sun bayyana cewa tana karatu a jami’ar Bayero da ke Kano.

Mace irin wannan tana da wahalar samu musamman idan aka kalli yadda take da kyau, ilimin addini da na boko ga kuma natsuwa wacce haddar da ke kanta ta samar mata.

Muna yi musu fatan alkhairi tare da yi musu addu’ar samun zuri’a dayyiba. Ga bidiyon malamin:

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button