Amfani da Medicated soap Yana kawo mace sanyin Gaba
A yau ɓangaren lafiya muna dauke da wani bayyani wanda shafin lafiya uwar jiki sunka wallafa a shafinsu akan matsalar Medicated soap wanda tana da illa sosai a wajen mata.
Amfani da medicated soap kamar su detol da septol soap yana kawo wa mace sanyin gaba.
Dalili shine: akwai wassu kwayoyin halitta a gaban mace masu amfani, amfanin su shine su bada kariya ga mace daga infection.
Idan ana yawan amfani da medicated soap yana iya kashe waɗannan kwayoyin hallitar masu amfani..
Me kuke tunani idan waɗannan kwayoyin hallitar suka mutu ?
~ ko wacce kwayar cuta idan yazo zai iya shiga ba tareda ya samu barazanar kariya ba…
A nan nasan mai karatu zai tambayi to su fa maza suma akawai
Har maza yawan amfani da medicated soap ba naku bane..
Akwai illa ga fata..
Martani mutane akan wannan rubutun suna cewa
@shehu mubarak suleiman yana cewa:
Shi gaban mace dama ai self-cleansing ne, wato Allah yayi masa baiwar wanke kan shi da kan shi ba tare da an tusa wani abu a ciki ba. Tusa wani abu a ciki ya kan wanke wasu kwayoyin cuta a cikin gaban, masu amfani sosai ga lafiyar ya mace.
@lafiya uwar jiki Ta ce Yes ma’ana hakane bayyaninsa.