Labarai

Jami’ar Maryam Abacha ta karrama atiku Abubakar ta sanyawa Wata Tsangaya Sunan Sa

A yayin Wani taro Mai cike da tarihi, Jam’iar Maryam Abacha American University ta Najeriya ta karrama Dan Takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP a zaben badi Atiku Abubakar, inda ta sanyawa wata Tsangaya sunan sa.AbdulRasheeth shehu mataimakin na musamman a fagen sada zumunta na Atiku Abubakar na kafafen sada zumunta na walafa

Ginin Tsangayar Mai suna Atiku Abubakar na dauke da kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa da sha’anin Mulki, Atikun ne da kan sa ya kaddamar da shi.

Jami'ar Maryam Abacha ta karrama atiku Abubakar ta sanyawa Wata Tsangaya Sunan Sa

A Taron kaddamarwar Wanda ya sami halartar manyan mutane a Kano, Wanda ya kafa Jam’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya jinjinawa Wazirin Adamawa, inda ya bayyana shi da wata mabubbugar ilimi da karfafa gwiwa ga matasan Najeriya. Yace Jam’iar da Atiku Abubakar ya kafa a Yola shi ne abinda ya sanya shi bude tasa Jami’iar a Maradi ta jamhoriyar Nijar, kuma da zai bude abokan huldar sa sun tura shi wurin Atiku domin samun shawarwari. Ya godewa tsohon mataimakin shugaban kasar bisa yadda ya Dora shi a hanya, inda yace Najeriya na bukatar mutum Mai kwarewa kamar Atiku Wanda yasa sha’anin ciki da Wajen Najeriya domin ci gaban kasa. Ya kuma bukaci matasa su Yi koyi da mutane irin Atiku da suka cimma nasarori a rayuwa.

A nasa jawabin, Dan Takarar na PDP Atiku Abubakar, yaja hankalin hukumar Jam’iar bisa wannan girmamawa. Ya kuma bada labarin yadda ya hadu da tsarin ilimin Amurka da kuma yadda yake kaunar sa. Yace banbancin dake tsakanin tsarin mulkin Amurka da sauran shi ne , suna bada damar yaye dalibai masu tunani, abin da ya basu damar mamaye fagen fasaha a duniya.

Ya kuma bada shawarar a Samar da ingantaccen tsarin manhajar ilimi da zata bawa daliban mu kwarewar da ake bukata don goga kafada da sauran sassan duniya.

A Wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban kasar ya Kai ziyara ga kasuwar Wayoyin salula ta Beruit dake Kano, inda ya jajantawa Yan kasuwar sakamakon iftila’in rushewar bene tare da rasa Rai guda. Ya kuma ya basu gudummawar naira miliyan 10.
Can a baya kuma ya bada gudummawar naira miliyan 50 ga yan kasuwar kantin kwari da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a Kano

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button