Labarai

Kyakkyawar baturiya ta iso Najeriya wurin saurayin ta, tana shirin yin wuff da shi

A ranar Asabar 2 ga watan Yuli, 2022 da misalin ƙarfe ɗaya na rana, wata baturiya ‘yar ƙasar Canada, Natasha, za tayi wuff da wani angon ta ɗan Najeriya mai suna Gift.

Jaridar Labarunhausa ta rahoto cewa baturiyar wacce ta haifi yaro ɗaya ta shigo Najeriya a cikin ‘yan kwanakinnan domin haɗuwa da masoyin na ta a karon farko wanda suka haɗu a shafin Instagram shekara ɗaya da ta gabata.

An nuna bidiyon lokacin da baturiyar ta shigo Najeriya

Masoyan biyu sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da baturiyar ta iso Najeriya yadda suka rungume juna cikin shaukin ƙauna.

Haka ma wani bidiyo da aka wallafa a TikTok ya nuna yadda suka fara hira kimanin shekara ɗaya da ta wuce.

Duk da sukar da tasha daga wurin masu amfani da yanar gizo kan cewa Gift kawai na amfani da ita ne domin samun katin zama ɗan ƙasar Canada, baturiyar ta cigaba da kare soyayyar dake a tsakanin su ta hanyar wallafa bidiyoyi masu kyau.

Natasha lokaci bayan lokaci tana sanya bidiyon yaron ta manhajar TikTok. Sai dai abinda baa sani ba shine ta taɓa aure ko bata taɓa aure ba.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

I_am_Mbuyi ya rubuta:

Dukkanin ku matasa ne masu jini a jika, kuna da damar da za kuyi rayuwa mai kyau a tare idan har za ku iya tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa.

FilipeDaCosta83 ya rubuta:

Za suyi aure, su tafi Canada, sannan da zarar ya samu zama ɗan ƙasa, zai rabu da ita. Idan kana tantama jira nan da shekara biyar ka gani.

A cewar bidiyon, matashin ya tura mata saƙo a Instagram, inda daga gaisuwar mutunci abu ya riƙiɗe ya koma abota inda daganan suka tsunduma cikin kogin soyayya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button