Labarai

Dalilin Da Yasa Na kafa Gidauniyar Tallafawa Mabuqata – Inji Rashida Mai Sa’a

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da Rashida mai sa’a, ta yi fice a wajen tallafawa marayu da sauran mabukata a gidaunaiyarta Mai Sa’a Charity kuma a karkashin wannan Gidauniyar tata mabukata masu yawa sun samu ‘yanci ta hanyar ba su ilimi da samar musu da lafiya da sauran abubuwan bukata inda take shiga lungu da sako don ganin ta warware matsalolin mabukata. A zantawarsu da wakilinmu Rashida Mai Sa’a ta yi bayani a kan tsawon lokacin da ta yi tana gudanar da Gidauniyar tata, da kuma yadda ta fara gudanar da harkokin nata har ma da nasarorin da ta samu. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance. 


To, Rashida za mu so ki sanar da masu karatu yadda a ka yi ki ka samar da Gidauniyarki ta Maisa’a Charity da kuma abubuwan da ki ke gudanarwa a gidauniyar? To, ita dai wannan gdauniya tawa ina ganin na kafa ta ne yau kusan shekaru takwas kenan. Kodayake a baya da na kafa ban yi mata suna ba, ina yin abubuwa ne haka na tamako sai na ga akwai bukatar na rinka tafiya da zamani, don haka sai na mayar da shi a matsayin Gidauniya, na yi mata suna na ci gaba da yin abubuwa da sunan Gidauniyar ina taimaka wa marasa karfi, idan mutum ba shi da lafiya na kai shi asibiti kuma nakan shiga asibiti duka na ji dakin yara masu yoyin fitsari ina kai musu tallafi kuma sai ya zama na bude abin na dauki ma’aikata da za mu rinka yin aiki da su, sai kuma na gano akwai mutanen da suke son tallafa wa jama’a. 


Sai dai ba su da kafar da za su bayar, wasu kuma suna son su yi tallafin amma ba su da kudin da za su yi, to a haka sai muka hadu wasu su bayar kuma wasu da ba su da hali bayarwa sai su zo mu tafi mu raba kayan tallafin da su. Ka ga sun yi da karfinsu. Muna shiga lungu da kauyuka kamar wajen ‘yan gudun hijira muna kai musu kayan abinci da kayan sakawa da magunguna, har muna yin gwaji na cutar HIB da kwayar polio mu hada kai da kungiyar lafiya, kuma muna kokarin gyara kamar saka rufin kwano da tabarmi da butoci har ma da fanka kuma muna samar da makarantun Islamiyya don akwai wani kauye da muka kai tallafi na sabulu da omo to akwai wata mata da ta tashi ta daga hannu ta ce ita ba burin da take da hsi ta kai shekara 40, amma ba ta iya fatiha ba, don haka suna son mu kawo musu malaman addini da za su rinka koyar da su. To a wannan waje a take muka nemi mai unguwa ya sahhale mana mu yi makaranta ta Islamiyya ta langa-langa, kafin mu samu damar da za mu gina musu. Haka kuma aka yi aka samar musu na zo cikin gari na samar musu da malamar da ake zuwa tana koyar da su. To yanzu an kusa shekara guda kenan ana ba su ilimi a yanzu har mun zama ‘yan’uwa da su. Har kayan miya za ka ga sun aiko min kwandon tumatur. To, a yanzu ya ya tafiyar da gidauniyar take idan kika kwatanta da ta baya? E, a yanzu an samu ci gaba sosai ka ga da ni kadai ce don abin d ana samu shi ne nake yin hidima da shi, amma yanzu da na samu mukamin gwamnati a matsayina na mai ba Gwamna shawara a kan harkar mata ka ga samun kudina ya karu, kuma ina bin manyan mutane wadanda ba za su iya fitowa da kansu su yi ba in bi ina kai wa mutane takard na neman taimako don akwai bukaar da z ata taso wadda ta fi karfinmu. Sai mu rubuta takarda mu kai wa masu hali, kuma ckin hikimar Allah duk inda muka je ba ma rasawa. 


A wannan aikin da kike yi kowanne mara lafiya ne kika samu wanda kika matsu ko ta halin kaka ki ga an samu taimako don ya samu lafya? To akwai wani yaro wanda na san maganarsa ta yadu a Kano har sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya je ya duba yaron za a yi masa aikin koda. Watarana mun dawo daga wani kauye wjaen rabon tallafi sai na ce mu bi ta sibitin Nassarawa don mu duba jikin yaron. Muka je muka tambaya mene ne matsalar sa? Aka ce za a yi masa dashen koda naira miliyan goma sha daya. Cikin ikon Allah da na zo na saka abin a cikin shafina ina jin sha biyu na dare na saka, amma karfe uku na dare sai ga wani mutum daga kasar Jamus ya ce na tura masa komai na asibitun da kuma aikin da za a yi masa, da kuma kudin da za a kashe a aikin, amma wani al’amari na Allah bayan mun je mun gama magana iyayensa sun ba da asusun ajiyarsu Allah ya yi wa yaron rasuwa, kuma mun kara samun wani mutum ana da ciwon koda yana da ciwon suga da HIB kuma yana da kansa ta cikin jini, to ana son a fita da shi zuwa Indiya, don yi masa magani, sia na sanar da wannan mutumin ga halin da wannan ake ciki kwanaki uku ya turo da miliyan bakwai sai aka shirya tafiya wannan mara lafiya sai da ya kai wata uku a indiya Allah ya sa ya rabu da ciwon duka, a yanzu mutumin yana cikin koshin lafiya, kuma kullum yana yi min fatan alheri. A yanzu ma da shi muke harkar raba kayan tallafi na gidauniyata. 



Don daga wannan ya kawo min wasu marasa lafiya an nema musu magani. Ko wane irin nasarori ki ka samu a rayuwarki ta b
angaren tallafawa jama’a da ki ke yi? To babbar nasara ita ce sa farin cikin zuciyoyi don a duk lokacin da tallafa wa jama’a na kan samu kaina cikin farin ciki, kuma na samu lambobin yabo da dama da aka karrama ni da su har ma London na je na karbi lambar girmamawa, kuma nan gaba kadan zan je kasar Jamus shi ya sa kullum muke buda abin don yanzu akwai kaya da muka dinka na ‘yanmata da yara wanda za mu kai Tudun Maliki gidan masu tabin hankali. Akwai ‘yanmata da smaari da uske bukata haka akwai wata uwar marayu da ita ma za mu kai mata baiwa yara don su yi hidimar maulidi don tunawa da haihuwar fiyayyen halitta. Wasu kungitoin idan suna neman tallafi na mara lafiya akan turo musu kudin ta asusun ajiyarsu ke ma haka ne? To haskiya ni ba haka ba ne, nakan tura asusun ajiyar ‘yan’uwa ko iyayen ma bukata ne, idan na tura nawa ka ga yau ba ka san yadda rayuwa za ta kasnace ba to idan ta Allah ta kasance sai abin ya zama da matsala, don haka ba na yin amfani da asusun ajiyata kuma duk kudin da muke samu ba ma amfani da shi a bukatar kanmu sai dai mu tura ga masu bukata. Daga karshe mene ne fatanki na karshe a game da wannan gidauniya taki? Fatana shi ne har ‘ya’yana da jikokina su gaji abin da nake yi kuma ina godiya ga dumbin jama’a da suke ba da gudunmuwa musamman Gwamnatin Kano da sauran jama’a

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button