Labarai

An Kama wani tsoho yana aikata Alfasha da Yar makwabcinsa inda yace yafi Shekara Goma yana Lalata

An kama wani mutum mai shekaru 57, mai suna Chidi Obieze a ranar Laraba bisa zarginsa da lalata wata yarinya ƴar shekara 10.

Mutumin wanda ya ce shi dan asalin Egbem Ozubulu ne a karamar hukumar Ekwusigo ta jihar Anambra, an kama shi ne a unguwar Oraifite da su ke makwabtaka, saboda yadda ya saba da lalata ƙananan yara.

Daga iƙirarin da ya yi a wani faifan bidiyo da aka nada, ya ce ya shafe shekaru 10 yana lalata ƙananan yara mata.

Mutumin da matasan Oraifite suka kama shi suka daure shi, ya roki a yi masa sassauci, inda ya ce a shirye ya ke ya daina idan har aka sake shi a halin yanzu.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Obiaze ya ce: “Ni ma ina son mata da suka manyanta, amma na fi son Ƙananan yara.

“Na yi wannan kusan shekaru 10 yanzu.”

Da aka tambaye shi ko me yake yi da yaran, sai ya ce, “ina taɓa ta ne kawai a lokacin da aka kama Ni. Kawai taɓa nake yi a farjin ta, aka kama Ni.

DAILY POST, duk da haka, ta kasa tantance abin da ya faru da mutumin daga bayan wannan bidiyon.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga inda aka miƙa mutumin ga ‘yan sanda a yankin bai haifar da da mai ido ba domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga samun nasarar samun layin wayar sa ba.

A wani labarin kuma: Hisbah A Zamfara ta yunƙuro kan yaƙi da Ƴan bindiga, ta haɗa hannu da NSCDC

Hukumar Hisbah ta jihar Zamfara ta ce za ta hada kai da jami’an tsaron farin kaya na Najeriya NSCDC a jihar Zamfara domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban Hukumar Alhaji Ashahabu Zoma ne ya bayyana haka, wanda ya jagoranci gudanarwar hukumar a ziyarar ban girma da ya kai ga Hukumar NSCDC.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button