Matar Da Ta Kashe Yaranta: Abin Da Ya Kamata A Duba Na Bincike ~Datti Assalafy
Hauwa’u matar da ta yiwa yaranta guda biyu yankan rago saboda mijinta zai kara mata kishiya kamar yadda ake yadawa, to ya kamata a duba wasu abubuwa na ka’idar binciken laifi irin wannan na kisan kai (Culpable Homicide) kafin a yanke mata hukunci ko a yadda ita ta aikata laifin, saboda wannan laifi ne da ba’a san yana faruwa ba bisa al’ada na zamantakewar ‘dan-adam
(1) Ko ta ha’inci mijinta ne tana dauko cikin shege na yaran a waje tana shigo masa dashi gida ta haife ba zata iya saka hannu ta yanka yaranta indai ita ta haifesu har guda biyu yankan wuka ba, zata iya kashe yaranta amma banda ta hanyar yankan rago, domin ko yaran da ake haifansu gidan karuwai su taso su girma suyi ciki su haihu gidan karuwai ba zasu iya aikata wannan ba, na farko binciken DNA ya taso anan, dole a bincika kwayar halittar jinin yaran da ubansu domin a gano nashi ne ko na wasu ne a waje
(2) Matsala na tabin kwakwalwa ko shafar aljanu ko shan miyagun kwayoyi zai iya sa ta aikata hakan, misali da ‘yan Boko Haram masu kunar bakin wake, basa iya aikatawa sai sun sha miyagun kwayoyi ya kawar da hankalinsu suna iya hallaka iyayensu da yaransu da kowa, sannan matsala na shafar Aljanu, domin daga ganin kalar wannan matar ba mai addini bace, lura da yanayin shigarta ba mai saka hijabi bace, da kuma yanayin kwayoyin idonta da alamar Aljanu a tare da ita, wannan sunanta Aljanu gate is free, ba za’a taba rasa ta da bakaken Aljanu a jikinta ba, akwai bukatar gabatar da kwararrun Malamai masu Ruqya su binciketa, sannan a kaita asibitin mahaukata su binciketa
(3) Idan bincike za’ayi; shi kansa mijin ya cancanta a kamashi da laifin rashin bawa yaransa kariya, sannan a bincikeshi a gano dalilin da ya sa matarsa ta harzuka har ta aikata laifin da ake zargin ta aikata, sannan budurwa ko bazawaran da yake shirin aura ko ya aura itama ya kamata a kamata, domin tana iya yiwuwa ita ta tura makisa su shirya manakisar da zata kawar da matar daga gidan domin ta samu kofar shigowa, domin ‘dan-adam wanda bai fahimci addini ba, bai da tsoron Allah babu abinda ba zai iya aikatawa ba don neman cikar burinsa a rayuwa
(4) An nuna mana hotuna har da na gawar yaran, amma to ina hoton wukar da matar tayi amfani dashi wajen yanka yaran?, Police Fingerprint Expert zasuyi bincike su gano tambarin fatar hannun matar ne a jikin wukar da aka yanka yaran ko kuma tambarin hannun wani ne ko wata?, saboda har yanzu ba’aji daga bakin matar ba tukunna
(5) Akwai bukatar Police Forensic Analysis akan wayar matar, za’a fara bincike kamar daga awanni 3 zuwa kafin ta aikata kisan yaranta da ake zargin ta aikata, akwai wani tracking da Police zasuyi akan nambar wayoyinta daidai lokacin da abin ya faru, domin a gano wasu lambobin waya da suke kusa ko suka gitta a kusa da nambar wayan matar da ake zargin ta kashe yaran nata, sannan abi diddigin kiran wayoyinta na wasu kwanaki da sakonnin da ta tura
(6) An saka mata miyagun kwayoyi masu rikitar da kwakwalwa a cikin abincinta ko abin shanta ta ci ko ta sha ba tare da saninta ba har ya kai ga ta aikata wannan danyen aiki? ko kuma ‘yar maye ce wato ‘yar kwaya?, suma jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) wato ‘yan Drugs, suna da nasu aikin na bincike
Don haka indai ba wannan bayani na bincike ya kammala ba to kada muyi saurin yanke hukunci a yanzu kam
Allah Ya sauwake