Kannywood

Ina da burin zama shugaban Nijeriya- Shuaibu lawan Kumurci

Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurari da mawakan masana’antar fim ta Kannywood kan abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 113, mun tattauna da tauraron fina-finan Hausa, Shu’aibu Lawan Ahmad wanda aka fi sani da Kumurci.

Jarumi Shu’aibu Lawan da aka fi sani da Kumurci ya ce yana da burika da dama a ransa, daga ciki akwai burinsa na son zama shugaban kasar Nijeriya duba da yadda ya ga lamurra na ta kara tabarbarewa.

Hakika ina da burika masu yawa, cika hada burina na son ganin na zama shugaban kasar Nijeriya duba da yadda nake son na ga na gyara abubuwan da suka dagule a kasar” in ji shi.

Shuaibu lawan Kumurci yace fim din dijan gala shine farkon film dinsa wanda abokinsa hafiz Bello yazo masa da cewa zai iya acting saboda daman majalisar su daya da hafiz Bello, Ali Nuhu da Tijjani. Sa’a nan fim din’ “UQubah” shine fim din da na samu sunan kumurci.

Ina da burin zama shugaban Nijeriya- Kumurci
Shuaibu kumurci Tare da Ali njhu

Wannan shine labarin haduwarmu da matata margayiya balaraba.

Farkon haduwar mu da balaraba shine nazo wani guri da ake kira el-duniya sai naga tana ta kallona already tasan dani nine ban san da ita ba, ni kuma sai na dan kiyaye kada tace na kureta da kallo amma naga duk abinda nake yi hankalinta yana kaina haka dai munka gama abinda muke a lokacin ina tare da abokaina su kwazaza,damisa da sinana ni kuma na hudunsu.

“Sai nake cewa naga wannan yarinyar tana ta kallona sai sinana yace ae tunda mu jarumai ne dole su kalle mu, bayan sati an kira muzo mu kashe wani a cikin fim din saboda shine aikinmu yarinyar nan sai ta sake zuwa tare da sani musa mai iska saboda shine ya kawota a motarsa sai ta nuna tana so tayi hoto dani, sai nace a’a saboda kina tare da abokina zaiji wani haushi.

Ina da burin zama shugaban Nijeriya- Kumurci
Shuaibu kumurci Tare Da matarsa margayiya Balaraba

Bayan wani lokaci tayi ta nema da hoton domin ta bani ashe tayi ta nemana daga nan sai Aisha dan kano tazo da cewa yarinyar nan kaji kaji nace a’a ban yarda ba.

“Saboda ina kallon matsayina a lokacin ina kallonta yadda naganta nasan banda abinda zata soni sai abokaina sunka ce a’a ae bata yiyuwa mutum ya nuna maka yana sonka kazo ka guje shi, ashe maganar har taje gidansu bayan naje sai babanta ke bani labarin cewa ae ita mamana domin sunan mahaifyarsa gareta cewa duk ya kawo fina finai na hausa idan akwai ni bata kalla sai tayi ta zagi da cewa shi wannan mai cutar da mutane dan Allah a daina kawo musu fim dinsa.

Sai baban yace kesan inda rana zata fadi tace miye inda rana zata fadi sai anka fasara mata da cewa kinka sani ko ki dawo kina son shi ko ki aureshi.

Tace Allah ya kiyaye wannan dan daba dan kaza shikenan ya wuce.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button