Kannywood

Rashin Lafiyar Mahaifina Ya Yi Tsanani, Amma Kaf Masana’antar Fim An Rasa Mai Tallafa Masa Inji Ibrahim Waragis

Malam Waragis dai ya dade yana shirya fina finai a masana’antar ta kannywood wanda a halin yanzu yake fama da matsanancin rashin lafiya na koda inda aka rasa Wanda zai taimaka da kudin da za’a wanke masa kodar duk cikin ‘yan film.
A yayin tattaunawar jaridar Dimokuradiyya  da Dan cikin malam waragis mai suna Ibrahim Wanda shi kadai Allah ya ba waragis din a matsayin Dan cikin sa ya shaida mana  cewar.

mahaifina yana fama da jinya mai tsananin gaske amma babu mai tallafa mana, abun mamaki harda masana’antar su duk da rawar daya taka a lokacin yana da lafiya.

Ya kara da cewan ciwon ya kai dole sai an masa wankin koda Sai dai Yaron ya bayyana cewar kwanakin baya da Ciwon yayi tsanani sosai Jarumi Ali Nuhu ya tallafa musu da dubu 25 haka kuma Sadik Sani Sadik ya basu dubu 35 bayan su babu wanda ya tallafa musu daga masana’antar da  Baban shi yake aiki.

Kazalika Yaron Waragis din yace Hajiya Zainab Ziya’u ta ba su dubu 220,h aka kuma kanwar jaruma Ummi Zee-zee, wato Haseena wadda ita ce Matar Dan Chana, ta ba su tallafi sosai wanda yawan kudin ya tasarma dubu 300.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button