Labarai

An kama wani yayi yarinya fyade tare da sanyamata barkono a gabanta

Advertisment

Wani Mutum Ya Gurfana A Gaban Kotu Bisa Laifin Cin Zarafin Wata Karamar Yarinya Da Barkono Kafin Yayi Lalata Da Ita Ya Kuma Jimata Raunuka

A ranar Larabar da ta gabata ne wani matashi mai suna Odili Chukwuka mai shekaru 35 ya gurfana a gaban wata kotun hukunta laifukan yara da jima’i da ke zamanta a Amawbia jihar Anambra bisa zargin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 17.

Wanda ake tuhumar wanda ya fito daga garin Aguluezechukwu a Aguata, jihar Anambra, yana fuskantar tuhume-tuhume tara da suka hada da yin lalata, cin zarafi ba bisa ka’ida ba, sata da kuma rauni a jiki.

Sai dai kuma mai laifin ya ki amsa laifinsa lokacin da aka karanta masa kunshin tuhumar.

Mai gabatar da kara, Insifekta Anayo Nwano, ya shaidawa kotun cewa an aikata laifukan ne a ranar 28 ga watan Yuli a Aguluezechukwu.

“Wadanda ake tuhumar da sauran su sun yi lalata da wata yarinya ‘yar shekara 17 ta hanyar tabawa da shafa mata barkono a al’aurarta.”

“Ya ci mutuncinta a cikin zuciyarta kuma ya ci zarafinta ba bisa ka’ida ba ta hanyar tube mata kaya tsirara, ya daure mata hannu da kafafu, ya yi mata bulala ya sanya mata barko a al’aurarta tare da yi mata rauni a jikinta.

“Ya kuma hana ta ‘yancinta tare da sace wayarta da jaka dauke da wasu kudade da ba a tantance adadin su ba,” in ji shi.

Alkalin kotun Majistare Genevieve Osakwe ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun ‘yan sanda tare da dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Satumba.

WANI LABARI:Dan fashi ne duk Jami’in Dake amsar kudi a hannun Al’umma ~ Sifetan ƴan sanda

 

Shugaban ‘Yan Sandar Najeriya, IGP Usman Alkali yace, Duk Jami’in Dan Sandan da aka gansa rike da Bindiga cikin Shirin aiki, Kuma Yana amsar kudi daga hannun Jama’a ba marabarsa da Danfashi, inji shi.

Babban Sifetan ya Cigaba da cewa, a duk lokacin da Wani yaga irin wannan Jami’in, Yana Kira cewa, su Saka na’urar daukar hoto, a Samar da hotonsa, kana a kaiwa caji ofis mafi kusa domin a hukunta shi.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button